Saturday 27 March 2010

Facebook | Tilin Shara a...

Facebook | Tilin Shara a...

Tilin Shara a Biranen Mu


Ban sani ba ko wani zai gane wannan tilin sharar dake wannan hotan. To wannan dai wata unguwa ce a birnin da yafi kowanne girma a nahiyar Afrika. Wato birnin da na fito, birnin da aka haife, Kano.

Kusan ta kowanne bangare Kano shine birnin da ya fi kowanne birni a Nigeria. Wannan ma shi ya sa ake masa kirari da: Kano, ko da mai ka zo an fika. Sai dai kuma tsakani da Allah, ba komai ne ya kamata a ce birni na, yafi saura akai ba.

Ba alfahari ba ne a ce birni na shi ya fi kowanne kazanta ko tarin shara a Nigeria ko Afrika. Idan na zo da baki ina yawo da su a garin nakan ji matukar kunya. A gaskiya ma, akwai unguwannin da bana bi da su.

Na yadda kan cewa yawan jama’a na taimakawa wajen taruwar shara a kankanin lokaci. To amma musun da nake san yi anan shine, ai idan aka samar da wata hanya kyak-kyawa, mai tsari, ta kwasar shara akan kari, ba tare da bata lokaci ba, to kuwa za’a rage afkuwar matsalar tarin shara a Kano.

A lokacin da nake korafin tilin shara a garin mu, sai na tuna cewa a gaskiya matsalar tarin shara a tsakiyar al’umma ba matsala ce da ta tsaya a Kano kawai ba. A’a!

Kusan ilahirin biranen arewacin Niigeriar da na je a shekarun nan na fama da matsalar shara. Sai dai a ce wasu sun fi wasu.

Tilin shara a tsakiyar al’umma na kawo barazana kala’kala ga bil adama. Alal misali saboda dankarewar sharar da ta hada da tsummokara, leda, bawawwaki, dusa, kashin awaki, takardu, kai da duk wani abu maras amfani, wadanda akan jigba akan magudanan ruwa, sauro ke cin karen sa ba babbaka. Sakamakon wannan kuwa itace cutar cizon sauro wato Malaria a turance.

Abun da kan bani mamaki kuma shine yadda zaka ga masu suyar kifi ko balangu sun soye-soye ko gashe-gashen su a dab da tilin sharar. Kuma mutane suna ta siya ba tare da tunani hakan na iya janyo musu cuttukar kamar su amai da zawo da Thypoid ba.

Haka kuma sai ka ga yara da matasa suna tsince-tsincen robobi ko rafta – kamar yadda ake cewa a Kanon – dan siyarwa.

Idan hukuma na da laifi, suma jama’ar unguwa da gari suna da nasu laifin. Menene ya sa ba za’a hada kai, a fitar da wani tsari da zai tabbatar da jama’a ba sa zubar da shara a ko ina ba sai inda hukuma ta shata? Me yasa mutane basu damu da kiwon lafiya da tsaftar muhallin su ba?

Mai yiwuwa wasu su ce ai matsalar shara kadan ce, akwai wadanda suka fi ta girma. Amma a nawa tunanin wannan ma matsala ce musamman tun da tana barazana ga lafiyar al’umma.

Me ya kamata mu yi akan matsalar shara a biranen mu? Zan so in ji daga duk mai shawara.

Sunday 21 March 2010

Ana Ga Yaki Suna Ga Kura


Babu shakka kasashe masu tasowa na fama da dimbim matsaloli. Mafi yawan wadannan matsaloli kuma mutane ne ke janyo su – ba wai Allah ne ke doro su ba. Kodayake dai kusan a kowanne lokaci mu kan danganta abubuwan mu ga kaddara, amma kuma wajibi mu kasance masu taya Allah kiwo.

Ina Kano a ranar da gobarar ta tashi a kasuwar kantin Kwari. Na isa kantin Kwarin bayan da mai aikowa da BBC rahotanni daga Kano, Yusuf Ibrahim Yakasai ya bugo mani waya jim kadan bayan misalin shida da rabi na safiya.

Koda na isa kantin Kwari sai na iske dubban mutane sun yi cincirundo, ana ta firmitsi-mitsi. Na ga wadanda nake zaton ‘yan kasuwa ne suna kici-kicin kwashe kayan su daga shagunan dake kusa da wadanda ke cin wuta – musamman ma dai gidan Labaran wanda a wannan lokaci yake ta ci da wuta.

Baya ga masu kokarin kwashe kaya, sai kuma ga ‘yan kallo. Wadannan sune mutanen da suka ba ni mamaki. Su wadannan mutane samari da manya, sun je wajen gobarar ne wai dan kashe kwarkwatar idanu. Yawan ‘yan kallon ya sanya an samu cunkoso a bisa ‘yar siririyar hanyar da ita ce masu motar kashe gobara za su bi.

‘Yan kallon ba su yi tunanin cewa gobara ba abar kallo ba ce, da kuma cewa suna saka rayuwar su da lafiyar su a cikin hadari. A yadda na ga ginin ke ci da wuta, kiris yake jira ya ruguzo kasa. Ina cikin wannan tunani sai na ji ana “ku gafara, ku gafara, ginin zai fadi”.

Sai rududu...jama’a suka fara gudu. Allah dai ya kiyaye firmitsi-mitsin bai kai ga jikkata ko hallakar kowa ba.

Wani abu da na lura da shi a lamarin gobarar kantin Kwarin kuma shi ne aikin tsarin ceto idan wata masifa ta auku a Nigeria. Ni dai har na bar wajen, motar kashe gobara kwaya daya kacal na gani (kamar yadda wannan hoto ya nuna). Kuma ban ga ta na feshin ruwa a lokacin da naje ba. Da na yi tambaya sai aka ce wai babu ruwa amma ana jira za’a kawo.

Bayan wani lokaci na bar wajen. An dai ce ruwa ya samu isa, kuma an samu kashe gobarar da ta fara ci tun karfe daya na safe har zuwa misalin bayan azahar – wato wajen sa’o’i 12-14 kenan. Ganin tsukukun wajen, Allah ne kawai ya takaita ta’adi da hasara.

Idan akwai masu lissafin gobarar kantin Kwarin da ta faru a wannan watan, to wajibi ne su yi nazari kan batutuwa da dama da nufin daukar darussa domin kiyaye gaba. Kadan daga wadannan su ne:

Ya kamata kayayyakin ceto da agaji kamar na kashe gobara su kasance a kowacce kasuwa ta yadda ba sai gobara ta tashi ba za’a shiga nemo mota da ruwan kashe ta?

Shin ginin kasuwannin mu ne irin na zamani ne ta yadda zasu kasance an samu raguwar masifu kamar gobara da ambaliyar ruwa?

Akwai hanyoyi masu fadi da za’a iya kaiwa ga kantina ba tare da masu aikin agaji ko ceto sun samu matsala ba?

Ya kamata jami’an tsaro kamar su ‘yan sanda su shiga aikin killace wajen da matsalar ta afku saboda hana ‘yan kallo cushe wajen?

Shin akwai wata hanya da za’a ragewa wadanda irin wannan masifa ta afkawa radadi wato ta hanyar basu tallafi? Domin kuwa a ganina idan ba wani ikon Allah ba, gobarar nan ta kantin Kwari zata kasance karshen wasu kenan.

Mai yiwuwa idan muka tunkari wadannan batutuwa mu taya Allah kiwo.

Allah ya kiyaye.

Monday 1 March 2010

Komai da Ruwanka


Bayani abune mai matukar mahimmanci ga kowanne dan Adam, ga kowacce al’umma, kuma ga kowacce kasa. Ingancin bayani kan baiwa mutum damar daukan matakai ko matsayar da suka dace a gareshi – abunda a turance ake kira “informed decision”. Misali idan baka da bayani akan abu, kana aka zo aka yi maka tambaya akan abunnan, to shaci fadi za ka yi, ko gaibu, ko kuma ka fadi abunda ba gaskiya ba.

Aikin ‘yan jarida shine nemo labarai komai dacin sa, sannan ka fada ba sani, ba sabo. Aikin jarida yana da ka’idoji da sharruda kamar kusan kowanne aikin kwararru. Alal misali BBC, kamfanin jaridar da ya fi kowanne suna a duniya, ya ginu akan wasu ginshikai: gaskiya, tsayawa a tsakiya wato babu goyon bayan wani bangare da kuma adalci –wato baiwa kowa hakkin sa. Watakila saboda tsayawa kan wannan manufa ta aikin jarida ne ya sa BBC ta yi fice a aikin jarida a duniya.

Tarihi ya nuna cewa a da, BBC ta kan dauki ma’aikatan da lallai ba ne a ce suna da takardar shaidar digiri. Amma yanzu saboda akwai gasa ta kowanne fanni har ma da a fannin aikin jarida, ya sa gidajen jarida kamar su BBC din neman wadanda ke da wani adadi na ilimi kafin a dauke aiki. Aikin jarida a duniya irin ta yanzu, wato mai saurin sauyi saboda ci gaba ta fannin fusaha, ya sa ana matukar bukatar gogewa muddin dai za’a ci gaba da kasancewa a gaban wadanda ake gasa da su a fagen aikin jaridar.

Ban san abunda ya yi tunani akai ba amma Malam Bashir Sule Kofar Sauri dan dandalin zumunta na BBC Hausa Facebook ya aiko mani sako kamar haka: “Hajiya ina da tambaya game da wannan profession din naku, wai yaya, ko sakandare mutum ya gama in dai ya shiga aikin jarida sai ya dunga kiran kan shi journalist. Ba wani matsayi da mutum sai yakai kafin ya kira kanshi journalist, koko yaya ne?

Na aikewa da Bashir, amsa inda na ce, “Haka yake a (wasu kasashe ciki har da) Nigeria mutanen da basu cancanci yin wani aikin ba, sai ka ga suna yi. Ga misali: kana bukatar takardar shaidar kammala karatu na musamman kafin ka fara harhadawa da siyar da magunguna. Amma a Nigeria kowa zai iya siyar da magani - har a tire mutane suke dauka, suna yawo da shi a ka. Kai dai kawai sai dai mu roki Allah ya yaye mana halin da muke ciki a kasar mu”.

Malam Bashir ya sake mai da mani da martani inda ya ce “haka yake sunan su doctors haka ma ake kiran su a Lagos. In ba ka ce doctor da karfi ba ma, ba zai juyo ba”.

To wannan matsala dai akwai ta a aikin jarida. Da akwai wadanda ba su da wata cikakkiyar shaidar karatu, amma su na aikin jarida. Har kamfanin jarida ma suke budewa. Ba wai ina cewa sai karatun ka ya kasance a fannin jarida ba, a’a. Za ka iya aikin jarida idan kana da digiri a wani fanni da ba aikin jarida ba amma kuma sai ka yi ta kwasa-kwasai daga kwararrun kamfanonin aikin jarida har ka zama gogaggen dan jarida. Alal misali BBC ba ta dagewa kan cewa sai kana da digiri a aikin jarida kafin a dauke ka aiki; amma kuma lallai sai mutum ya kasance yana da digiri.Da zarar ka zo BBC, za’a baka horaswa abunda kuma har ka bar gidan, ba za ka daina yi ba. A shekaru kusan 18 din da na yi ina aiki da BBC, na yi kwasa-kwasai da suka haura 40 – tun daga kwas na sa’o’i, zuwa na makonni. Hatta ma a makon jiya sai da nayi na rabin wuni.

Tambayar da Malam Bashir Kofar Sauri ya yi mani ta sa ni tunani kwarai. Na lura cewa lallai idan muna san kasar mu ta ci gaba to wajibi ne mu baiwa harkar ilimi mahimmanci. Ingataccen ilimi shi zai tabbatar da ingantacciyar rayuwa da kuma ingantacciyar makoma. Shi zai kawo kwararru da gogaggun ma’aikata. A takaici ilimi zai taimakawa mutum ya samu ci gaba, sannan al’ummar sa ma ta samu ci gaba.

A karshe bari in koma inda na faro; wato batun mahimmancin bayani. Ban sani ba ko dai aikinmu na ba da labarai da bayani - ba sani ba sabo – ne ya sa Malam Bashir ya yi mani tambaya. Allahu a’alam. Abunda dai na yi imani da shi, shi ne, tambayar sa ta sa ni sake tunani kan mahimmancin ilimi ga al’ummata ta yankin arewacin Nigeria, wadda kuma dukkanin alkaluma ke nuni da cewa ta na baya kwarai da gaske, idan aka kwatanta da yankin kudancin Nigeria.

Facebook | Akwai bukatar amsa...

Facebook | Akwai bukatar amsa...