Wednesday 28 April 2010

Matasa da Bangar Siyasa a Nigeria


Yanzu haka an fara shiga yanayin siyasa a Nigeria wato yayinda ake shirin gudanar da zabukan shekara mai zuwa.

Siyasa na da mahimmanci a kowacce kasa ta duniya dake bin tarafkin democradiyya. Dalili kuwa shine siyasar tsarin democradiyya na baiwa jama’a damar zabar wanda suke ganin ya dace da su, kuma wanda zai biya masu bukatun su da kuma share masu hawaye.

Jama’a kan ba da goyon baya ga wanda suka yi imanin zai wakilce su – kuma wakilci na gari – ba wanda zai je dan wakiltar kan sa ba. Ta yaya jama’a ya kamata su tabbatar da cewa sun zabi na gari ba zaben tumun dare ba?

Mai yiwuwa sai nan gaba zamu tattauna wannan batu. Amma ina so na yi a wannan sharhi ne akan siyasar banga.

Tun bayan da Nigeria ta koma tsarin democradiyya yau shekaru sama da goma ‘yan siyasar kasar ke amfani da matasa domin cimma manufofin su na siyasa. Ba laifi ba ne ‘yan siyasa su nemi goyon bayan matasa. Misali a baya-bayan nan, kuri’a da goyon bayan matasan Amruka ta taimaka gaya wajen nasarar shugaba Barack Obama a 2008.

Abunda yake laifi shine amfani da matasa a matsayin ‘yan bangar siyasa domin samun nasara a zabe. A zabukan da suka wakana a baya ‘yan siyasa a Nigeria na baiwa matasa kudi, inda su kuma sukan sayi kwaya da sauran ababen sa maye da makamai, suna bi suna razana abokan hamayya da sauran jama’a.

Kamar yadda na gani a wannan hoto dake kan wannan shafi (wanda na dauka sa’ilin da na kai ziyara Bauci a watan jiya), rikici kan rincabe tsakanin ‘yan bangar siyasa. Akan yi fito-na-fito tsakanin ‘yan bangar ‘yan siyasar. Wani lokaci a ji munanan raunuka, a wasu lokuta a rasa rayuka. Wannan abun takaici ne.

Shin matasan nan da suke bari ana amfani da su dan cimma manufar zabe, duk da cewa sun san ‘yan siyasa zasu yi watsi da su, da zarar sun yi nasara, sun san ciwon kan su kuwa? Suna da masaniya kan cewa ‘yan siyasa basu damu da su ba illa kawai sun mai da su tamkar matattakala ce da suke takawa domin “cin zabe” ko ta halin kaka?

Amsar da nake san sani itace: ta yaya ne matasa zasu jajirce su ki yarda ana amfani da su a matsayin ‘yan bangar siyasa a bisa kudi kalilan – wadanda akewa kallon marasa mutunci a Nigeria - lamarin da ka iya sanadiyyar hasarar rayukan su da ci bayan kasar su?

Sunday 4 April 2010

Facebook | Yaushe Za Su Gane?

Jiki Magayi - Talaka na Mutuwa a Rikice-Rikice


Rikicin addini da na siyasa sune manyan labarun dake janyo fargaba ga Edita ko shugaban kafar yada labarai. Alal misali wajibi ne na tabbatar da cewa mun bada labarin rikice-rikicen addini da kabilancin ba tare da nuna san zuciya ga kowanne bangare ba. Haka ma rikicin siyasa.

Babban abunda na lura da shi a aikina shine a Nigeria kusan kashi casa’in cikin dari na rikice-rikicen da ake yi, manya ne suke ta da su. Manya sun hada da wasu masu kudi, da wasu malaman addini na Musulunci ko Kirista, da wasu ‘yan siyasa.

Tun lokacin da Nigeria ta kama bin hanyar democradiyya a 1999, kasar ta yi fama da rikice-rikicen addini da kabilanci daban daban. Tun daga rikicin OPC Shagamu, Kano, Zangon Kataf, Tibi, Yalwan Shandam har zuwa na baya-bayan nan, wato su Boko Haram, Kala Kato da kuma rikice-rikicen Jos.

Masu bincike sun yi ittifakin cewa manya na da hannu a wadannan rikice-rikice. Suka ce wannan ne ma ya sa aka ki hukunta kowa.

A hirar da na yi da shi a BBC Hausa, tsohon sarkin Gwandu Alhaji Mustapha Jakolo ya yi tambaya mai mahimmanci. Ya ce “kin taba jin wani babban mutum, ko shugaban addini na Musulmi ko na Kirista da aka kashe, ko kuwa ‘ya’yan su? A kullum aka tashi masifa a Nigeria, hasara na tsayawa ne ga talakawan kasar.”

Wannan maganar haka take. Da na je Jos a kwanannan, ilahirin hasara – ta rai da dukiya – ta kare ne kan talaka. Wannan ne ma ya sa ni tambayar: me yasa talakawa ba zasu gano cewa wasu na amfani da su ba ne domin cimma wata manufa? Wani da wahala, wani da riba – shine abunda ke faruwa.

Abunda zan so in ji daga gareku shine: yaushe ne talakan Nigeria zai koyi darasi? Yaushe ne zai daina yarda wasu manya suna amfani da shi, kuma a karshe hasara rai ko ta dan abunda suka mallaka ta komo kansu? Yaushe zai ce, “idan kana so muyi kashe-kashe bamu ‘ya’yan ka mu je tare”?

Lokaci yayi da talaka zai jajirce ya ki karbar ‘yan tsirarun Nairori dan biyan bukatar wasu da a zahiri basu damu da su ba, domin iyalan su na turai su na karatu ko shakatawa da kudaden da ake zargin sun kwashe na su talakawan.

Hausawa dai suka ce jiki magayi.