Thursday 23 December 2010

Shugabannin Afrika Na Karen Tsaye ga Democradiyya


Zabuka a nahiyar Afrika na neman zama wani abu daban. Abubuwan da yanzu haka ke faruwa a kasar Cote d’Ivoire abubuwa ne da ke tayar da hankali ga duk wani mai san ganin ci gaba a nahiyar Afrika, abubuwa ne dake tayar da hankali ga ma’abota tsarin mulki irin na democradiyya.

Bayan shafe shekaru 10 yana mulki a kasar ta yammacin Afrika, da kyar da jibin goshi Laurent Gabgbo ya amince ya gudanar da zaben kasa baki daya. Dama dai kada mu manta cewa kasar ta yi fama da yaki da tashe-tashen hankula, lamarin da sai da kasashen duniya da majalisar dinkin duniya suka yi wurjanjan kafin su kawo karshen sa.

A watan jiya an yi zabe. Kuma ‘yar manuniya ta nuna. Abunda kuwa ta nuna shine cewa Alhassan Ouattara ne ya lashe zaben. Amma sai me zai faru?

Sai shugaban da ya shirya zaben Laurent Gabgbo yayi kememe ya ce ba zai sauka daga mukami ba, bayan kuwa hukumar zaben kasar mai zaman kanta ta bayyana sakamakon da ya nuna Alhassan Ouattara ne ya yi nasara.

Laurent Gabgbo ya rantsar da kansa a matsayin zababben shugaban kasa. Shima kuma Alhassan Ouattara ya bayyana kansa a matsayin sabon shugaban kasar ta Cote d’Ivoire.

Kasashen duniya sun yi Allah wadai da karan-tsayen na Mr Gagbo, kuma kawo yanzu tuni har an fara zub da jini, abunda kuma Allah kadai ne ya san inda lamarin zai tsaya.

Babban abunda lamarin na Cote d’Ivoire ke nunawa shine shugabannin Afrika basu san menene democradiyay ba. Basu yadda cewa jama’a zasu iya sauya shugabanninsu ta hanyar dangwala dan-yatsa bisa katin zabe ba.

Yana kuma nuna cewa shugabannin Afrika ‘yan kama-karya ne, wadanda ba sa mutunta bukatun jama’arsu. Dama a ce ma suna yiwa kasa aiki ne, suna kawo kyakkyawan ci gaba ga rayuwar talakawa, to dama da sauki. To amma mulki a nahiyar abune na “ramin-kura”.

Kada kowa ya raba daya biyu cewa abunda ya faru a Cote d’Ivoire ba zai iya faruwa a sauran kasashen Afrika ba. Ko shakka babu hakan zai iya faruwa a kowacce kasa a nahiyar; domin kuwa launin shugabannin – abunda Hausawa ke cewa ne – duka kanwar ja ce.

Sai dai manyan tambayoyi su ne: har ya zuwa yaushe ne jama’ar Afrika, da talakawa zasu ci gaba da amincewa da mulkin kama-karya? Har zuwa yaushe ne shugabanni za su ci gaba da taka bayin Allah saboda suna takama da karfin iko da kujerar da suke kai?

Mai yiwuwa talaka ba zai iya ba, kodai saboda tsoro, ko saboda rashin sanin ‘yancin kansa. Sai dai idan su ba zasu iya ba, Allah zai iya musu.

A karshe ina mai tsinkayen wani lokaci a gaba, da idan ance shugaba yayi irin abunda ke wakana a Cote d’Ivoire yanzu, zai ranta a na kare, ya ce “ku rufa mani asiri”.

Allah ya nuna mana wannan lokaci ko mulkin adalci da gaskiya ya wanzu a nahiyar mu. Allah ya kawo mana karshen karen-tsayen da shugabanni ke yiwa tsarin democradiyya a Afrika.