Friday 17 June 2011

Yaya Za'a Warware Matsalar Boko Haram

Matsalar Boko Haram, matsala ce da kowa yake jin tsoron yin sharhi akai. Dalili kuwa shine suna ganin muddin suka yi magana watakila ‘yan Boko Haram din su kai masu hari. Amma kuma a matsayinmu na ‘yan jarida dole ne mu yi tsokaci dangane da abubuwan da ke faruwa a kasarmu da nufin neman hanyoyin warware wadanda muke ganin matsaloli ne.

Boko Haram ta somo asali yau kusan shekaru 2, inda ake daukar jihar Borno dake arewa maso gabashin Nigeriar a matsayin hedikwatar su. Ana ganin aikace-aikacen ‘yan kungiyar da cewa kokari ne na ganin an kaddamar da Shari’ar Musulunci a Nigeria.

Hare-haren da Boko Haram ke kaiwa sun tsananta ne bayan kashe shugabansu
Mohammed Yusuf da jami’an tsaron Nigeria suka a Yulin 2009. Tun a wancen lokacin ne ‘yan Boko Haram suka sha alwashin daukar fansa tare da yaki da duk wadanda suke ganin makiyin su ne.

Yanzu haka dai abu yayi abu. Boko Haram na kai hari ta ko ina, duk dai a kokarin cimma manufofinsu. A lokacin da ya kai ziyara Amurka, Shugaban Nigeria Goodluck Jonathan ya bayyana a makon da ya gabata cewa yana neman a tattauna da ‘yan Boko Haram din, da nufin kawo karshen tashe-tashen hankulan da ake samu a wasu sassan kasar. Sai dai bayan kalamin na sa, sai aka ambato shugaban rundunar ‘yan sandan Nigeria Hafiz Ringim yana yin barazana ga ‘yan Boko Haram yana mai cewa karyar su ta kusan karewa.

Ana dai bayyana cewa wai wannan furuci ne ya tunzura ‘yan Boko Haram suka kai hari a hedikwatar ‘yan sandan Nigeria dake Abuja. Daga bisani kungiyar ta fitar da sanarwa tana mai daukar alhakin harin bam din da yayi sanadiyyar hasarar rayuwa da dukiya.

To yanzu da aka zo wannan matsaya, ta yaya za’a tunnkari matsalar Boko Haram?

Ni dai har yanzu banga wani wanda a yanzu ya lashi takobin cewa yana da wata cikakkiyar masaniya ba. Amma a matsayin mu na masu sharhi kan al’amuran da suka shafi kasar mu wajibi ne mu nemi ansa ga wasu mahimamman tambayoyi. Wadannan kuwa sune:

Menene ya janyo matsalar Boko Haram? Su wanene ‘yan Boko Haram? Ta yaya za’a fara tattaunawa da su domin neman sulhu? Yaya shugabannin Nigeria zasu kasance masu tausayin jama’ar su ta yadda jama’a zasu daina yi musu kallon makiya? Yaya ‘Yan Nigeria suke san makomar kasarsu a gajeren lokaci da kuma a shekarun gaba ya kasance? Wadanna matakai za’a dauka na zahiri ba abunda Fulani suke cewa “foululu” kawai ba?

Bayan mun yi wadannan sai mu hada da addu’ar neman Allah ya kawo mana zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar mu Nigeria.

Wednesday 15 June 2011

EFCC KO KYANWAR LAMI


Yau shugabar hukumar yaki da laifukan da suka danganci ta’annati da dukiyar jama’a a Nigeria wato EFCC ta yi bikin cika shekara 8 da kafuwa. Shugabar ta zayyana irin kokarin da hukumar ta su ta yi, wajen zakulo wadanda ta kira miyagun da suke wawaso da dukiyar jama’a.

Hukumar ta kara da lasafta sunayen manyan mutane, musamman ma tsoffin ministoci da gwamnoni da wasu ‘yan kasashen waje da suke da uwa a gindin murhu- wato manyan jami’an gwamnatin Nigeria - a matsayin shaidar kokarin da suke yi na sa kafar wando guda da duk wannda ya yiwa dukiyar Nigeria karan tsaye.

Lallai wannan ba karamin abu bane a kasar da cin hanci ya zame mata jini da tsoka. Ko a cikin ‘yan kwanakin nan sai da jami’an tsaro suka yi artabu da tsohon kakakin majalisar wakilan kasar Dimeji Bankole kafin su kama shi a makon jiya. Hukumar EFCC din na zargin Bankole da barnatar da kudin da suka haura Naira biliyan 40.

A gaskiya dai duk da kokarin da EFCC ta ce tana yi, jama’ar Nigeria na ci gaba da yi mata kallon wata wadda ke da manufa ta karkashin kasa. Allal misali a yanzu haka da akwai wadanda suke zargin cewa wai ana tuhumar Bankole ne saboda ya ja ragamar ‘yan majalisar da suka sauya dokar zaben kakakin majalisa. Shi kuma wannan sauyi da majalisar ta yi, shi ya kai ga wancakalar da shirin karbi-in-karba, lamarin da ya batawa jam'iyyar PDP rai.

To, ko ma dai wane kallo ake yiwa EFCC, mutane masu yawa na ganin, kamata yayi hukumar ta daina kwakwazo, ta kama mutum, kana sai a ji shiru. A madadin haka idan aka kama mutum, sai a kaishi kotu, a yanke masa hukunci, sannan a bayyanawa jama’a hukuncin da aka yanke masa, saboda ya zama darasi ga saura. Har yanzu kalilan ne a cikin manyan mutanen da EFCC ta bayyana sunayen su aka gurfanar da su gaban kuliya kana aka yanke musu hukunci. So tari maganar shiriricewa take yi kawai.

A karshe muddin dai EFCC na san ta yaki ta’annati da dukiyar jama’ar Nigeria, to wajibi ne ta tabbatar ta ga karshen zargin wawason da ake yiwa mutane, sannan ta bayyanawa duniya hukuncin daurin da aka yiwa mutum. Baya ga wannan sai kuma sauran hukumomi su buga sitamfi akan mutumin nan da aka yankewa hukuncin, da cewa: muddin aka kama ka da laifi, kana aka hukunta ka bisa laifin satar dukiyar bayin Allah, to kuwa kayi sallama da rike mukami a Nigeria, komai kankantarsa.

Muddin ba’a yi haka ba, kowa zai ci gaba da kwasar ganima saboda ya san cewa bayan an kamala hayaniya a kafofin yada labarai, zai kwana kalau. Watakila bayan ‘yan watanni ya tsaya takarar mukami, kuma a ganshi mirsisi wai yana rike da matsayin mai yin doka a kasa, ko ya zama shugaban al’ummar da ya taba cuta a matakin jiha ko kasa.

A yayinda ta cika shekara 8 da kafuwa, dole EFCC ta guji kasancewa Kyanwar Lami.