Friday 4 October 2013

Babban Abu Da Ya Sosa Mani Rai

Yau shekara biyu da wata uku kenan cif, rabon da na yi rubutu a wannan mattara tawa – Almajira. Na jima ne kuwa ban yi rubutun ba saboda matukar sauye-sauye na halin rayuwa ta yau da kullum. Wannan sauye-sauye kuwa sun hada da kai komo a wurin aiki da gida. Tun sanda na rubuta tunani na karshe a wannan dandali abubuwa da dama sun sauya. Babba daga cikin su shine na ajiye aikina a wajen da mutane da yawa suka fi sanina wato BBC, bayan na shafe kusan shekaru ashirin ina aiki da wannan kafar yada labaran ta Ingila mai dadadden tarihi. Dama dai Hausawa suka ce komai na duniya mai karewa in banda ikon Allah. Lallai tun sannan na komo kasata Nigeria domin gannin yadda zan ci gaba da ba da gudunmawata ga al’ummata. A yanzu haka dai ina aiki a hukumar tsare-tsaren taswirar birnin Abuja wato Abuja Geographic Information Systems (AGIS). A yau wani babban abu da ya sosa mani rai ya faru. Shugabannin kungiyar Murya Talaka, Shiyyar Jihar Kano – wato Jiha ta, sun yo tattaki, suka kawo mani ziyara. Muraya Talaka sun gabatar mani da shaidar yabo kan abunda suka kira taimakar da na yi “wajen bunkasa harshen Hausa da dabi’un Hausawa da kuma bugu da kari kusantar Talaka”. Sun yi bayani dalla-dalla a game da abunda ya sa suka ga na dace na karbi wannan lambar yabo. A takaice dai sun zayyane mani tarihi na nan take! A karshe dai matasan nan sai da suka sa na zubar da hawaye. Ashe duk abunda kake yi ana kallon ka? Na yi masu godiya, na karbi lambar yabon su. Kuma na ba su shawarwari a game da yadda na ke ganin ya kamata mu ci gaba da yin gwagwarmaya domin kare marasa karfi a kasarmu. A karshe sun bakaci na samu lokaci duk da yawan aikina, na koma rubutu a mattarar bayanai na Almajira, saboda a cewar su, suna ganin wannan waje tamkar wajen daukar darasi. Ni kuma na amsa da cewa zan kokarta. Toh, gashi kuwa cikin hakuncin Ubangiji na yi rubuta na farko a dandalin Almajira a cikin watanni 27. Alhamdulillah! A sharhina na gaba zan yi tsokaci kan Babban Taro na Kasa (National Conference) wanda ‘yan kungiyar Muryar Talaka suka nemi jin ra’ayi na, da kuma ko yana da dangantaka da talaka. Allah Ya ba mu Sa’a, amin!