JAMILAH TANGAZA
Matattarar ra'ayi, da tunani kan al'ummaran yankin Arewa, da Nigeria da sauran sassan duniya.
Friday, 4 October 2013
Babban Abu Da Ya Sosa Mani Rai
Yau shekara biyu da wata uku kenan cif, rabon da na yi rubutu a wannan mattara tawa – Almajira. Na jima ne kuwa ban yi rubutun ba saboda matukar sauye-sauye na halin rayuwa ta yau da kullum.
Wannan sauye-sauye kuwa sun hada da kai komo a wurin aiki da gida. Tun sanda na rubuta tunani na karshe a wannan dandali abubuwa da dama sun sauya.
Babba daga cikin su shine na ajiye aikina a wajen da mutane da yawa suka fi sanina wato BBC, bayan na shafe kusan shekaru ashirin ina aiki da wannan kafar yada labaran ta Ingila mai dadadden tarihi.
Dama dai Hausawa suka ce komai na duniya mai karewa in banda ikon Allah. Lallai tun sannan na komo kasata Nigeria domin gannin yadda zan ci gaba da ba da gudunmawata ga al’ummata.
A yanzu haka dai ina aiki a hukumar tsare-tsaren taswirar birnin Abuja wato Abuja Geographic Information Systems (AGIS).
A yau wani babban abu da ya sosa mani rai ya faru. Shugabannin kungiyar Murya Talaka, Shiyyar Jihar Kano – wato Jiha ta, sun yo tattaki, suka kawo mani ziyara. Muraya Talaka sun gabatar mani da shaidar yabo kan abunda suka kira taimakar da na yi “wajen bunkasa harshen Hausa da dabi’un Hausawa da kuma bugu da kari kusantar Talaka”.
Sun yi bayani dalla-dalla a game da abunda ya sa suka ga na dace na karbi wannan lambar yabo. A takaice dai sun zayyane mani tarihi na nan take! A karshe dai matasan nan sai da suka sa na zubar da hawaye. Ashe duk abunda kake yi ana kallon ka?
Na yi masu godiya, na karbi lambar yabon su. Kuma na ba su shawarwari a game da yadda na ke ganin ya kamata mu ci gaba da yin gwagwarmaya domin kare marasa karfi a kasarmu.
A karshe sun bakaci na samu lokaci duk da yawan aikina, na koma rubutu a mattarar bayanai na Almajira, saboda a cewar su, suna ganin wannan waje tamkar wajen daukar darasi. Ni kuma na amsa da cewa zan kokarta.
Toh, gashi kuwa cikin hakuncin Ubangiji na yi rubuta na farko a dandalin Almajira a cikin watanni 27. Alhamdulillah!
A sharhina na gaba zan yi tsokaci kan Babban Taro na Kasa (National Conference) wanda ‘yan kungiyar Muryar Talaka suka nemi jin ra’ayi na, da kuma ko yana da dangantaka da talaka.
Allah Ya ba mu Sa’a, amin!
Friday, 15 July 2011
Ga Tashin Bama-Bamai ga Watan Ramadan
Halin da ake ciki yanzu haka a wasu yankun nan Arewacin Nigeria musamman ma Maiduguri ya kai abunda zamu ce “Inna Lillahi wa inna ilaihir rajiun”. Tashe tashen hankula sakamakon tashin bama-bamai da kuma samamen da ake kaiwa kan wadanda ake zaton yan kungiyar Boko Haram ne sun sanya matsanancin tsoro da fargaba a zukatan jama’a.
Ana ta muhawara kan yaya aka yi har aka kai wannan mummunan hali da ake ciki. Ni a ganina wannan ihu ne bayan hari. A madadin tambayar yaya aka yi aka kai haka. Kamata yayi a maida hankali kan yadda za’a samo maslaha domin kawo karshen wannan hali da ake ciki.
Sai dai kuma ko wannan ma ba karamar tambaya ba ce. Shin yaya ake ganin za’a iya magance matsalar? Ta ina za’a faro? Shin tattaunawa ya kamata ayi? Idan tattaunawa ce tsakanin wa da wa za’a yi? Kuma idan za’a yi tattaunawar su wanene zasu wakilci gwamnati, su wanene zasu wakilci ‘yan kungiyar ta Boko Haram?
A jiya an rawaito kungiyar tuntubar juna ta Arewa wato Arewa Consultative Forum ta na cewa zata baiwa shugaban Nigeria Goodluck Jonathan shawara kan yadda ta ke ganin ya kamata a tunkari matsalar ta Boko Haram.
Sai dai a wani lamari tamkar arashi, a yau sai kungiyar matasan Arewa wato Arewa Youth Forum suka fitar da wata sanarwa suna masu kakkausar sukan dattawan na Arewa. Suka ce ai dattawan basu da hurumi, halarci ko iyawa a game da yadda za’a warware matsalolin Arewa. Kungiyar ta ce ai tun da farko su dattawan Arewan ne suka jefa yankin cikin mummunan halin fatara da jahilcin da ake ciki. Amma yanzu kiri da muzu, sun zo su na maganar magance matsalar.
To lallai dai masifar da ake ciki a yankin Arewa ta Nigeria ba jiya ko shekaranjiya ta samo asali ba. Matsala ce da ta jima tana ci, can daga karkashi. A shirin BBC Hausa a Karkara na Maris 2009, na jagorancin ‘yan jaridar BBC Hausa inda muka ganewa idanuwan abubuwan da suka saka mu hawaye. A shirin BBC Hausa a Karkara na karshe na bayyana cewa Arewacin Nigeria na zaune akan bam wanda a kowanne lokaci zai iya tashi.
A wanncen lokaci wasu sun ce muna yiwa kasa mugun alkaba’i. Abun takaicin shine, sun kawar da idanun su daga halin talauci, rashin aikin yi, shaye-shayen miyagun kwayoyi, da watangaririyar da ‘ya’yan bayin Allah ke yi a yankin. A karshe ga halin da muke ciki a yau.
To babban jawabi na a wannan sharhi, shine, kamar kowa, ina yin roko na cewa yayinda watan ibada mai tsarki na watan Ramadan yake karatowa, shugabanni da ‘yan kungiyar Boko Haram, su dubi girma Allah Subhanu wata’ala, su nemi hanyar kawo zaman lafiya, hanyar da za’a wanzar da adalci tsakanin al’umma. Wannan shine kadai zai kawo zaman lafiya mai dorewa.
Friday, 17 June 2011
Yaya Za'a Warware Matsalar Boko Haram
Matsalar Boko Haram, matsala ce da kowa yake jin tsoron yin sharhi akai. Dalili kuwa shine suna ganin muddin suka yi magana watakila ‘yan Boko Haram din su kai masu hari. Amma kuma a matsayinmu na ‘yan jarida dole ne mu yi tsokaci dangane da abubuwan da ke faruwa a kasarmu da nufin neman hanyoyin warware wadanda muke ganin matsaloli ne.
Boko Haram ta somo asali yau kusan shekaru 2, inda ake daukar jihar Borno dake arewa maso gabashin Nigeriar a matsayin hedikwatar su. Ana ganin aikace-aikacen ‘yan kungiyar da cewa kokari ne na ganin an kaddamar da Shari’ar Musulunci a Nigeria.
Hare-haren da Boko Haram ke kaiwa sun tsananta ne bayan kashe shugabansu
Mohammed Yusuf da jami’an tsaron Nigeria suka a Yulin 2009. Tun a wancen lokacin ne ‘yan Boko Haram suka sha alwashin daukar fansa tare da yaki da duk wadanda suke ganin makiyin su ne.
Yanzu haka dai abu yayi abu. Boko Haram na kai hari ta ko ina, duk dai a kokarin cimma manufofinsu. A lokacin da ya kai ziyara Amurka, Shugaban Nigeria Goodluck Jonathan ya bayyana a makon da ya gabata cewa yana neman a tattauna da ‘yan Boko Haram din, da nufin kawo karshen tashe-tashen hankulan da ake samu a wasu sassan kasar. Sai dai bayan kalamin na sa, sai aka ambato shugaban rundunar ‘yan sandan Nigeria Hafiz Ringim yana yin barazana ga ‘yan Boko Haram yana mai cewa karyar su ta kusan karewa.
Ana dai bayyana cewa wai wannan furuci ne ya tunzura ‘yan Boko Haram suka kai hari a hedikwatar ‘yan sandan Nigeria dake Abuja. Daga bisani kungiyar ta fitar da sanarwa tana mai daukar alhakin harin bam din da yayi sanadiyyar hasarar rayuwa da dukiya.
To yanzu da aka zo wannan matsaya, ta yaya za’a tunnkari matsalar Boko Haram?
Ni dai har yanzu banga wani wanda a yanzu ya lashi takobin cewa yana da wata cikakkiyar masaniya ba. Amma a matsayin mu na masu sharhi kan al’amuran da suka shafi kasar mu wajibi ne mu nemi ansa ga wasu mahimamman tambayoyi. Wadannan kuwa sune:
Menene ya janyo matsalar Boko Haram? Su wanene ‘yan Boko Haram? Ta yaya za’a fara tattaunawa da su domin neman sulhu? Yaya shugabannin Nigeria zasu kasance masu tausayin jama’ar su ta yadda jama’a zasu daina yi musu kallon makiya? Yaya ‘Yan Nigeria suke san makomar kasarsu a gajeren lokaci da kuma a shekarun gaba ya kasance? Wadanna matakai za’a dauka na zahiri ba abunda Fulani suke cewa “foululu” kawai ba?
Bayan mun yi wadannan sai mu hada da addu’ar neman Allah ya kawo mana zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar mu Nigeria.
Boko Haram ta somo asali yau kusan shekaru 2, inda ake daukar jihar Borno dake arewa maso gabashin Nigeriar a matsayin hedikwatar su. Ana ganin aikace-aikacen ‘yan kungiyar da cewa kokari ne na ganin an kaddamar da Shari’ar Musulunci a Nigeria.
Hare-haren da Boko Haram ke kaiwa sun tsananta ne bayan kashe shugabansu
Mohammed Yusuf da jami’an tsaron Nigeria suka a Yulin 2009. Tun a wancen lokacin ne ‘yan Boko Haram suka sha alwashin daukar fansa tare da yaki da duk wadanda suke ganin makiyin su ne.
Yanzu haka dai abu yayi abu. Boko Haram na kai hari ta ko ina, duk dai a kokarin cimma manufofinsu. A lokacin da ya kai ziyara Amurka, Shugaban Nigeria Goodluck Jonathan ya bayyana a makon da ya gabata cewa yana neman a tattauna da ‘yan Boko Haram din, da nufin kawo karshen tashe-tashen hankulan da ake samu a wasu sassan kasar. Sai dai bayan kalamin na sa, sai aka ambato shugaban rundunar ‘yan sandan Nigeria Hafiz Ringim yana yin barazana ga ‘yan Boko Haram yana mai cewa karyar su ta kusan karewa.
Ana dai bayyana cewa wai wannan furuci ne ya tunzura ‘yan Boko Haram suka kai hari a hedikwatar ‘yan sandan Nigeria dake Abuja. Daga bisani kungiyar ta fitar da sanarwa tana mai daukar alhakin harin bam din da yayi sanadiyyar hasarar rayuwa da dukiya.
To yanzu da aka zo wannan matsaya, ta yaya za’a tunnkari matsalar Boko Haram?
Ni dai har yanzu banga wani wanda a yanzu ya lashi takobin cewa yana da wata cikakkiyar masaniya ba. Amma a matsayin mu na masu sharhi kan al’amuran da suka shafi kasar mu wajibi ne mu nemi ansa ga wasu mahimamman tambayoyi. Wadannan kuwa sune:
Menene ya janyo matsalar Boko Haram? Su wanene ‘yan Boko Haram? Ta yaya za’a fara tattaunawa da su domin neman sulhu? Yaya shugabannin Nigeria zasu kasance masu tausayin jama’ar su ta yadda jama’a zasu daina yi musu kallon makiya? Yaya ‘Yan Nigeria suke san makomar kasarsu a gajeren lokaci da kuma a shekarun gaba ya kasance? Wadanna matakai za’a dauka na zahiri ba abunda Fulani suke cewa “foululu” kawai ba?
Bayan mun yi wadannan sai mu hada da addu’ar neman Allah ya kawo mana zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar mu Nigeria.
Wednesday, 15 June 2011
EFCC KO KYANWAR LAMI
Yau shugabar hukumar yaki da laifukan da suka danganci ta’annati da dukiyar jama’a a Nigeria wato EFCC ta yi bikin cika shekara 8 da kafuwa. Shugabar ta zayyana irin kokarin da hukumar ta su ta yi, wajen zakulo wadanda ta kira miyagun da suke wawaso da dukiyar jama’a.
Hukumar ta kara da lasafta sunayen manyan mutane, musamman ma tsoffin ministoci da gwamnoni da wasu ‘yan kasashen waje da suke da uwa a gindin murhu- wato manyan jami’an gwamnatin Nigeria - a matsayin shaidar kokarin da suke yi na sa kafar wando guda da duk wannda ya yiwa dukiyar Nigeria karan tsaye.
Lallai wannan ba karamin abu bane a kasar da cin hanci ya zame mata jini da tsoka. Ko a cikin ‘yan kwanakin nan sai da jami’an tsaro suka yi artabu da tsohon kakakin majalisar wakilan kasar Dimeji Bankole kafin su kama shi a makon jiya. Hukumar EFCC din na zargin Bankole da barnatar da kudin da suka haura Naira biliyan 40.
A gaskiya dai duk da kokarin da EFCC ta ce tana yi, jama’ar Nigeria na ci gaba da yi mata kallon wata wadda ke da manufa ta karkashin kasa. Allal misali a yanzu haka da akwai wadanda suke zargin cewa wai ana tuhumar Bankole ne saboda ya ja ragamar ‘yan majalisar da suka sauya dokar zaben kakakin majalisa. Shi kuma wannan sauyi da majalisar ta yi, shi ya kai ga wancakalar da shirin karbi-in-karba, lamarin da ya batawa jam'iyyar PDP rai.
To, ko ma dai wane kallo ake yiwa EFCC, mutane masu yawa na ganin, kamata yayi hukumar ta daina kwakwazo, ta kama mutum, kana sai a ji shiru. A madadin haka idan aka kama mutum, sai a kaishi kotu, a yanke masa hukunci, sannan a bayyanawa jama’a hukuncin da aka yanke masa, saboda ya zama darasi ga saura. Har yanzu kalilan ne a cikin manyan mutanen da EFCC ta bayyana sunayen su aka gurfanar da su gaban kuliya kana aka yanke musu hukunci. So tari maganar shiriricewa take yi kawai.
A karshe muddin dai EFCC na san ta yaki ta’annati da dukiyar jama’ar Nigeria, to wajibi ne ta tabbatar ta ga karshen zargin wawason da ake yiwa mutane, sannan ta bayyanawa duniya hukuncin daurin da aka yiwa mutum. Baya ga wannan sai kuma sauran hukumomi su buga sitamfi akan mutumin nan da aka yankewa hukuncin, da cewa: muddin aka kama ka da laifi, kana aka hukunta ka bisa laifin satar dukiyar bayin Allah, to kuwa kayi sallama da rike mukami a Nigeria, komai kankantarsa.
Muddin ba’a yi haka ba, kowa zai ci gaba da kwasar ganima saboda ya san cewa bayan an kamala hayaniya a kafofin yada labarai, zai kwana kalau. Watakila bayan ‘yan watanni ya tsaya takarar mukami, kuma a ganshi mirsisi wai yana rike da matsayin mai yin doka a kasa, ko ya zama shugaban al’ummar da ya taba cuta a matakin jiha ko kasa.
A yayinda ta cika shekara 8 da kafuwa, dole EFCC ta guji kasancewa Kyanwar Lami.
Monday, 16 May 2011
Zaben 2011: Wancakalar da Babbar Dama
Zaben Nigeria na 2011 ya zo, ya tafi, ya kuma bar baya da kura. Babban makasudin wannan kura kuwa itace burin da jama’a suka dauka suka dorawa shugaban hukumar zaben da aka nada da zummar gudanar da zabuka masu inganci a kasar wato Farfesa Attahiru Jega, da kuma cewa a bana zasu yi amfani da kuri'arsu a matsayin babbar dama ta zabar wadanda zasu fish-she su daga halin la-haulan da suke ciki.
Kafin nada Jega 'yan Nigeria, da ma duniya gabakidaya, sun yi ittifakin cewa zabukan da aka yi a kasar a shekarun 2003 da 2007 ba wani abu bane, illa bankaura. Masu sa idanu kan wadancen zabukan sun bayyana cewa sune mafi muni a tarihin jefa kuri’a a Nigeria. Masu fafutukar wanzar da democradiyya a ciki da waje sun ta kokawar ganin an sauya tsarin zabe a Nigeria ta yadda zasu kasance ingantattu. Shi kansa shugaban da aka ce shi ya lashe zaben na 2007, marigayi Umaru Musa Yar’adua ya amince kan cewa lallai akwai bukatar yin gyara.
Saboda haka, bayan kasashen duniya musamman Amurka sun hurawa Nigeria wuta sai shugaba Goodluck Jonathan ya kawo Attahiru Jega a matsayin wanda zai gudanar da ingantattun zabuka a kasar. Sakamakon sunan da yayi a jami’a a matsayin “dan akida” da “taurin kai” sai jama’a suka ce, to zabe mai nagarta zai yiwu a Nigeria.
Sai dai tun sannan masu sharhi kan al’amuran siyasa a Nigeria kamar Dakta Junaidu Mohammed suka bayyana shakkunsu dangane da hakan. Suna masu cewa ai gyara ba zai yiwu idan mutun daya ne tak yake da manufar yin sa ba. Masu irin wannan ra’ayi sun dage kan cewa muddin dai ana san gyara, to wajibi ne Jega ya kori ma’aikatan hukumar zaben kasar INEC wadanda suka yi aiki a karkashin tsohon shugaban hukumar wanda ake yiwa kallon mazambaci wato Farfesa Maurice Iwu. Hakan dai bai faru ba.
A karshe dai ‘yan Nigeria sun kama hanyar jefa kuri’a ranar asabar 2 ga Afrilu, amma sai me? Ana tofa bisimillah, sai kwatsam, aka ba da sanarwar an dage zaben zuwa mako na gaba. Tun daga sannan ne gwiwowin jama’a da dama suka yi sanyi. A dan wannan lokaci an yi zargin kama manyan motoci makare da takardun zabe, da cewa sun yi sama ko kasa. Haka kuma jam’ian tsaro suma sun ta yin kalamai da suka ci karo da juna wadanda tun daga sannan jama’a suka ce, an ya kuwa?
Allah cikin ikonsa an yi zaben a haka – cikin zarge-zarge da fargaba, da tashe-tashen hankali, da abubuwan da ba zasu fadu ba.
Sai dai babban abunda ya fito wanda kuma shine babban abun takaici a wannan zaben shine yadda aka yi amfani da kudi, da kayan masarufi kamar sabulun wanka da shinkafa da taliyar Indomie, kiri-kiri a bainar jama’a, ba kunya, ba tsoro, dan jan hankalin masu zabe su zabi jam’iyyar da ke rabon kudin da kayan masarufin.
Abun bakin ciki shine, talauci da mutuwar zuciya sun yi tasiri, inda jama’a suka sa kafa suka shure damar da suke da ita ta kawo sauyi. A karshe sun zabi wadanda suka basu kudin da zai biya masu bukatar ‘yan kwanaki kilalan, a madadin wadanda ake ganin zasu kawo gyara na zahiri a kasa.
Wannan gajeren tunani ne a bangaren talakawa. Ba su tuna cewa wadanda suka basu kudin nan ba sune wadanda suka sa kafa suka dannan su cikin kuncin da suke ciki. Ba su tuna cewa kudin nan da aka dauko aka sammu su, dama nasu ne ba, wanda kuma da sune ya kamata a samar musu da wuta da ruwa da asibi da makarantu, amma aka ki yin hakan, sai da zabe yazo aka dan guzutso aka basu domin su mayar da yawu.
To a karshe talakawan Nigeria, da taimakon wadanda suka jefa su cikin kangin wahalar da suke ciki, sun wancakalar da damar da suka samu a 2011. Abunda yayi saura shine ko wadanda suka zaba a bana zasu fitar dasu daga matsanancin halin rayuwar da suke ciki ko a’a?
Da yace an ce Allah ya na baiwa al’umma shugabanni irin jama’arta, fatan mu kawai yanzu shine Ubangiji, Allah ya cece mu, Ya kawo mana sauyi tun daga cikin zukatanmu, mu kanmu, wanda kuma a karshe shi zai kaimu ga samun adalan shugabanni da zasu ciyar da kasar mu gaba.
Tuesday, 5 April 2011
Kancal A Shirin Zaben Nigeria
Zaben Nigeria na ci gaba da jan hankali a ciki da wajen kasar saboda dalilai da yawa. Kuma yanzu, fiye da kowanne lokaci, na yi imanin cewa duk kokarin mutum na kawo gyara a kasarmu, sai wasu sun yi kokarin kawo cikas, ko yin kancal!
Kowa dai ya san Profesa Attahiru Jega shugaban hukumar zaben Nigeria wato INEC, mutum ne mai akida. Kuma idan ya dage kan abu, ba’a iya tankwara shi.
Allah dai ya kai shi INEC, kuma tun sannan wasu suke cewa mai yiwuwa saboda akidarsa a samu ingantattun zabuka a Nigeria. Sai dai kuma wasu na cewa shi kadai ba zai iya kawo gyara ba. Inda masu musun farko ke cewa ai shugabanci na iya sauya na kasa. Ni ma ina daga cikin wadanda suka yi wannan fata.
Sai dai yayinda ni da sauran abokan aikina a BBC muka shirya kawowa ‘yan Nigeria rahotannin zaben da aka shirya yi a 2 ga watan Afrilu, sai kwatsam rahotannin matsaloli. A karshe dai an dage zabukan.
Dage zabukan sakamakon cikas din da aka samu abu ne da ya girgiza mutane da yawa. Sai dai mafi yawan ‘yan Nigeria na ci gaba da baiwa Jega goyon baya, suna masu cewa muddin dai zabukan zasu kasance na fisabilillahi, to ai dage su ba wani ba ne.
Ana dai ta hasashe da zarge-zarge cewa akwai wasu da suka hadiyi layer cewa zabukan nan ba zasu yi nasara ba ko ta halin hakaka saboda dalilan san-kai ba na san kasa ba. Idan haka ne Allah ya yi maganinsu domin bayin Allah.
A karshe ya zaman wajibi jam’ar Nigeria su jajirce wajen tabbatar adalci da samun shugabanni na gari.
Subscribe to:
Posts (Atom)