Matattarar ra'ayi, da tunani kan al'ummaran yankin Arewa, da Nigeria da sauran sassan duniya.
Sunday, 28 February 2010
Kiwon Lafiya a Arewacin Nigeria
A shirin BBC Hausa na safiyar yau an yi wani labari da ya taba ni sosai. Labarin shine na wasu iyaye mata dake dawainiya da 'ya'yan su dake da cutar amosanin jini wato “sickle cell” a turance. Dan jaridar BBC Nura Mohammed Ringim yayi hira da wata mace Hajiya Ba'adiya Magaji wadda dan ta ya rasu shekaru ukun da suka shige, yana mai sheharu talatin da biyar a duniya. Ita kuwa Hajiya Umma Tukur Unguwar Sarki ta na da yara 7 wadanda dukkanin su ke fama da amosanin jini. Ta ce “kafin wata 9 suke nuna alamun ciwon, kuma su na bukatar abincin mai kyau, a kullum su na cikin rigar sanyi saboda ba sa san sanyi, ba sa san wahala”. Wannan uwa ita ce ke kici-kici domin tabbatar da yaran ta suna cikin yanayin da zai hana ciwon ya tashi, abunda ake kira da turanci "crisis” kamar yadda ta shaida.
Watanni biyu da suka shige ni ma wata aminiya ta a Kano ta hadu da rashi sakamakon wannan cuta. Mahmud Kyauta dan aminiyar ta wa ya rasu yana mai shekaru 19 a duniya. Zai shiga jami’a a bana amma sai ciwo ya tashi, aka kai shi asibiti a Kano, cikin ‘yan sa’o’i kadan Allah yayi masa cikawa.
A matsayi na na uwa, na ji wa aminiyar tawa. Domin rashin da mai shekaru 19 a duniya ba karamin abu bane. Na yi ta kokarin ba ta magana da nufin kwantar mata da hankali...dadin abun, a gida, arewacin Nigeria, dangi da makobta kan taimaka a irin wannan lokaci mai wahala. Kodayake dai imani da Allah shine ma babban kushin dake tausasa zuciya.
Sai dai abunda na fahimta shine duk da hanyoyin samar da bayanai na zamani, ga kuma uwa-uba radiyo, har yanzu jama’a a yankin arewacin Nigeria suna da karancin sani ko ilimi kan wannan cuta, wadda ko shakka babu ke ragargazar iyaye da yara.
Amosanin jini in ji masana, cuta ce da ake gada daga iyaye. A takaice matsale ce dake hana zagayawar iska Oxygen a jinin dan Adam. Wannan rashin zagaye na Oxygen a jini kan haifar da ciwo mai tsanani ga mai cuta. Ciwon kan tashi ne musamman idan mutum ya na fama da mura, ko wata ‘yar larurar ko kuma idan ma yayi wani aiki da ya jigata shi.
Masana suna cewa amosanin jini kan kawo lalacewar wasu mahimman injinan dake motsa jikin bil Adama kamar hanta, koda, huhu, zuciya da fatsarmama – abunda kuma suke janyo matsanancin ciwo a kasusuwa jiki. Masu amosanin jini kan yi saurin kamuwa da wasu cututtukan na daban saboda gaukuwar jikin su ba ta da karfi – ma’ana suna da saurin laulayi.
Daga jerin wadannan matsaloli zaka fahimci cewa duk iyayen da Allah ya baiwa yaro ko yara masu fama da amosanin jini, to lallai jidali ya same su.
Anan Birtania akwai babbar kungiya ta masu fama da kuma kula da cutar amosanin jini. Bayanai daga shafin su na intanet ya nuna ba sa kasa a gwiwa wajen gudanar da ayyukan da suka hada da ilmantarwa, wayar da kai, tarukan karawa juna sani, kafa gidauniya dan gudanar da ayyukan bincike kan cutar da dai sauransu. Bayanan kungiyar suka kuma ce babban abunda suka yi imani da shi shine, duk masu cutar amosanin jini na da ‘yancin a basu kulawar da ta kamace su. Suka kuma ce ba sa nuna kyama ko banbanci dan kai “dan kasa ne” ko a’a; ko kuma dan jinsin ka daban da na turawa.
Wannan abun sha’awa ne kwarai, kuma ya sa ni na yi tunani a game da labarin da BBC Hausa suka bayar na kokarin da kungiyoyi irin wadanda aka yi rahoto akan su a yau suke yi a Arewa, wajen samar da yanayi kwatankwacin abunda na karanta a shafin intanet din kungiyar amosanin jinin Birtania.
Amma babban abunda ya sanyaya mun jiki shine sanin cewa harkar kiwon lafiya a Nigeria musammman ma a Arewa din ta na cikin halin da bai dace ba. Muna fama da karancin likitoci, kayayyakin aiki, magunguna da ma dakunan shan magani a yankunan karkara. Haka kuma saboda taluci ya yiwa jama’a katutu, so tari ma iyaye hakura suke yi da kai yara asibiti. Abunda ya ta’azzarar lamarin shine masu fama da cutar amosanin jini na bukatar abinci mai gina jiki saboda kara masu kuzari da rage masu yiwuwar kamuwa da cuttuka. A zahiri dai jama’a na fama da abunda zasu ci sau daya ma a rana. Kididdigar Majalisar Dinkin Duniya ta shekarar 2007 na cewa kashi 70 cikin 100 na ‘yan Nigeria na rayuwa a kasa da dalar Amruka guda a rana wato Naira 140.
Tambayoyi anan sune: yaya jama’ar yankin arewacin Nigeria zasu tunkari matsalar cututtuka ba wai kawai amosanin jini ba, a’a har ma da sauran cuttuka barkatai da jama’a – yara da manya – ke fama da su? Yaya mahukunta zasu samar da ‘yancin jama’ar su na ba su kiwon lafiyar da ya kamace su a matsayin su na ‘yan Adam da kuma ‘yan kasa? Hakkin wanene ya tabbatar da cewa hukumomi sun cika aikin su na kare hakkin jama’a, tare da sauke nauyin dake kansu? Su kuma al’ummar mu wace rawa zasu iya takawa? Ta yaya zasu taimakawa kansu wajen samun hakkin su na ingantaccen kiwon lafiya? Shin mazaje na bayar da tallafi ga matan su, ko kuwa suna sakarwa matan duk nauyi da wahalhalu ta yadda a wasu lokuta matan ke rasa inda zasu saka kan su? A game da cuta amosanin jini, suna sane da cewa idan suka yi gwajin jini kafin su yi aure zasu iya kaucewa samun yaran da zasu kasance masu fama da cutar?
A tunani na wadannan kadan ne daga cikin dinbim tambayoyin da ya kamata mu yi kokarin amsawa wajen tunkarar cutar amosanin jini da sauran cututtuka a Arewacin Nigeria.
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
Ranki ya dade, gaskiya ne wannan tana daya daga cikin cututtukan dake addabar yara da iyayen su (musamman iyaye mata).Tabbas yana da muhimmanci asamar da kulawa ga wadanda ayanzu wannan cuta ke addabar su. Amma kuma yana da matukar muhimmanci mahukunta su kawo wani tsari wanda zai zama anyi awon jini kafin auratayya. kuma iyaye dasu kansu mata su gane suyi kokari kada su ringa zama idanuwan su sun rufe da so wajen neman aure su ringa karfafa awon jinin tsakanin su da masoyan su kafin yin aure.Sannan bayan haka, ina ganin har a addinance ma ba zai zama laifi ba in har aka gane yiwuwar yaran da za'a haifa su zama masu wannan cuta su ma'aurata su tsayar da haihuwa tsakanin su.
ReplyDeleteAbubakar A. Usman,
Kuala Lumpur, Malaysia.