Matattarar ra'ayi, da tunani kan al'ummaran yankin Arewa, da Nigeria da sauran sassan duniya.
Monday, 1 March 2010
Komai da Ruwanka
Bayani abune mai matukar mahimmanci ga kowanne dan Adam, ga kowacce al’umma, kuma ga kowacce kasa. Ingancin bayani kan baiwa mutum damar daukan matakai ko matsayar da suka dace a gareshi – abunda a turance ake kira “informed decision”. Misali idan baka da bayani akan abu, kana aka zo aka yi maka tambaya akan abunnan, to shaci fadi za ka yi, ko gaibu, ko kuma ka fadi abunda ba gaskiya ba.
Aikin ‘yan jarida shine nemo labarai komai dacin sa, sannan ka fada ba sani, ba sabo. Aikin jarida yana da ka’idoji da sharruda kamar kusan kowanne aikin kwararru. Alal misali BBC, kamfanin jaridar da ya fi kowanne suna a duniya, ya ginu akan wasu ginshikai: gaskiya, tsayawa a tsakiya wato babu goyon bayan wani bangare da kuma adalci –wato baiwa kowa hakkin sa. Watakila saboda tsayawa kan wannan manufa ta aikin jarida ne ya sa BBC ta yi fice a aikin jarida a duniya.
Tarihi ya nuna cewa a da, BBC ta kan dauki ma’aikatan da lallai ba ne a ce suna da takardar shaidar digiri. Amma yanzu saboda akwai gasa ta kowanne fanni har ma da a fannin aikin jarida, ya sa gidajen jarida kamar su BBC din neman wadanda ke da wani adadi na ilimi kafin a dauke aiki. Aikin jarida a duniya irin ta yanzu, wato mai saurin sauyi saboda ci gaba ta fannin fusaha, ya sa ana matukar bukatar gogewa muddin dai za’a ci gaba da kasancewa a gaban wadanda ake gasa da su a fagen aikin jaridar.
Ban san abunda ya yi tunani akai ba amma Malam Bashir Sule Kofar Sauri dan dandalin zumunta na BBC Hausa Facebook ya aiko mani sako kamar haka: “Hajiya ina da tambaya game da wannan profession din naku, wai yaya, ko sakandare mutum ya gama in dai ya shiga aikin jarida sai ya dunga kiran kan shi journalist. Ba wani matsayi da mutum sai yakai kafin ya kira kanshi journalist, koko yaya ne?
Na aikewa da Bashir, amsa inda na ce, “Haka yake a (wasu kasashe ciki har da) Nigeria mutanen da basu cancanci yin wani aikin ba, sai ka ga suna yi. Ga misali: kana bukatar takardar shaidar kammala karatu na musamman kafin ka fara harhadawa da siyar da magunguna. Amma a Nigeria kowa zai iya siyar da magani - har a tire mutane suke dauka, suna yawo da shi a ka. Kai dai kawai sai dai mu roki Allah ya yaye mana halin da muke ciki a kasar mu”.
Malam Bashir ya sake mai da mani da martani inda ya ce “haka yake sunan su doctors haka ma ake kiran su a Lagos. In ba ka ce doctor da karfi ba ma, ba zai juyo ba”.
To wannan matsala dai akwai ta a aikin jarida. Da akwai wadanda ba su da wata cikakkiyar shaidar karatu, amma su na aikin jarida. Har kamfanin jarida ma suke budewa. Ba wai ina cewa sai karatun ka ya kasance a fannin jarida ba, a’a. Za ka iya aikin jarida idan kana da digiri a wani fanni da ba aikin jarida ba amma kuma sai ka yi ta kwasa-kwasai daga kwararrun kamfanonin aikin jarida har ka zama gogaggen dan jarida. Alal misali BBC ba ta dagewa kan cewa sai kana da digiri a aikin jarida kafin a dauke ka aiki; amma kuma lallai sai mutum ya kasance yana da digiri.Da zarar ka zo BBC, za’a baka horaswa abunda kuma har ka bar gidan, ba za ka daina yi ba. A shekaru kusan 18 din da na yi ina aiki da BBC, na yi kwasa-kwasai da suka haura 40 – tun daga kwas na sa’o’i, zuwa na makonni. Hatta ma a makon jiya sai da nayi na rabin wuni.
Tambayar da Malam Bashir Kofar Sauri ya yi mani ta sa ni tunani kwarai. Na lura cewa lallai idan muna san kasar mu ta ci gaba to wajibi ne mu baiwa harkar ilimi mahimmanci. Ingataccen ilimi shi zai tabbatar da ingantacciyar rayuwa da kuma ingantacciyar makoma. Shi zai kawo kwararru da gogaggun ma’aikata. A takaici ilimi zai taimakawa mutum ya samu ci gaba, sannan al’ummar sa ma ta samu ci gaba.
A karshe bari in koma inda na faro; wato batun mahimmancin bayani. Ban sani ba ko dai aikinmu na ba da labarai da bayani - ba sani ba sabo – ne ya sa Malam Bashir ya yi mani tambaya. Allahu a’alam. Abunda dai na yi imani da shi, shi ne, tambayar sa ta sa ni sake tunani kan mahimmancin ilimi ga al’ummata ta yankin arewacin Nigeria, wadda kuma dukkanin alkaluma ke nuni da cewa ta na baya kwarai da gaske, idan aka kwatanta da yankin kudancin Nigeria.
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
Wato na dade ina tunani kwarai da gaske akan kasa ta Najeriya. wato tun shekaru dubbai da suka wuce, lokacin masana na Girka kamar su Plato da almajirin sa Aristotle sun karfafa maganar ilimi da sani a tsakanin mutane na kowace al'umma in har ana so abubuwa su tafi yadda ya kamata. Haka nan, addinai na sama dukkan su musamman addinin Musulunci sun karfafa muhimmancin Ilimi da sani akan dukkan abinda muke yi ko zamu yi.Duk kasar da ayau ta cigaba ko take kokarin cigaba wannan shine abinda suka rike kuma suka bawa muhimman ci. Amma a Najeriya zaka samu, abin takaici, musamman a arewa, mutum dan karfin hali yayi kundun bala ya afka cikin abinda bashi da wata masaniya ko kadan koda kuwa wannan abinda yake yi barazana ce ga al'umma baki daya...Allah ya sawwake
ReplyDeleteAbubakar Abubakar Usman,
Kuala Lumpur, Malaysia.