Wednesday, 15 September 2010

Kashe-Kashen Gilla a Nigeria: Yaya Za Mu Yi da Ranmu?


Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un. Wannan tashin hankali da ake ciki a Nigeria, ubangiji Allah Ka yi mana maganin sa. A matsayin mu na ma’aikatan aikin watsa labarai, wannan makon ya kasance maras dadi. Maras dadi, saboda rahotannin kashe-kashe da daukar rai a kasar da muka fi maida hankali akanta a aikin na mu, wato Nigeria.

Ranar litinin a cikin shirin BBC Hausa na rana Yusuf Ibrahim Yakasai ya kawo wani rahoto wanda a cikinsa yake cewa an hallaka wasu mutane biyar, 'yan gida daya, a cikin daren lahadi. Wasu mutane ne da ba a shaida ko su wanene ba, suka shiga wani gida, a rukunin gidajen dake unguwar Kundila dake kan titin Gidan Zoo, a birnin Kano, suka yanka magidancin mai suna Garba Bello, mai kimanin shekaru hamsin da biyar, tare da matarsa, da kuma 'ya'yansa ukku.

Mun ji yadda yayar matar gidan da aka yanka, tana bada labarin yadda ‘yar-uwar ta da aka yanka din ta buga mata waya tana neman dauki. Amma kuma suna cikin magana sai wayar ta katse. Abunda yasa take jin a wannan lokacin ne maharan suka farma ‘yar uwar ta ta.

Ana cikin wannan jimamin kuma, a ranar talata sai muka ji Nurah Ringim yana hira da wata mata tana kuka, tana shash-sheka, tana maida yadda wasu mutane da ba’a san ko su wanene ba, suka shiga gidan su, suka harbe mai gidanta har lahira.

Marigayi Malam Abdullahi Muazu dai babban jami'in hukumar EFCC, mai yaki da masu yiwa tattalin arzikin Najeriya zagon kasa ne. Hukumar EFCC ta danganta kisan nasa da hare-haren da tace ana kaiwa jami'anta a halin yanzu.

Ana cikin yin haka sai Abba Katsina ya aiko mana da rahotan wani lamari da ba’a saba gani ba a arewacin Nigeria, inda wani matashi dan shekaru ashirin da biyu, ya kashe kansa da kansa. Matashin mai suna Murtala Ibrahim - wanda aka ce makarancin Al-Kur'ani ne - ya kashe kan nasa ne ta hanyar ratayewa. An tsinci wata takarda kusa da gawar tasa, inda ya rubuta cewa, ya kashe kan nasa ne, domin ya kawo karshen zaman da yake yi na rashin aikin yi.

Ko shakka babu, wadannan labarai masu ta da hankali ne ga duk mai hankali. Domin kuwa suna nuni da mummunan halin da aka shiga a kasar mu Nigeria. Mummunan hali ta kowanne fanni: fannin tsaro, fannin imani, fannin hankali da dai sauransu.

Yanzu haka babu wani mahaluki a Nigeria da zai iya cewa ya shige a afka masa, a hallaka shi ko wani nasa. Jama’a suna cikin matsananciyar fargaba.

A kasashen da suka ci gaba hukumomi da jami’an tsaro suna kare rayukan jama’a. Amma a Nigeria, harin ma harda su jami’an tsaron ake kaiwa baya ga jama’ar gari.

Tambaya anan shine, wai me ya kawo wannan halin lahaula da Nigeria take ciki? Laifin wanene? Yaushe ne ‘yan Nigeria zasu samu fita daga cikin masifar da suke ciki a kasar su?

BBC Hausa zata tattauna wannan batu a shirin “Ra’ayi Riga” na wannan makon. Sai ku kasance da BBC Hausa.
http://www.bbc.co.uk/hausa/

4 comments:

  1. so wannan sakacin hukuma ne don a lokacin mulkin buhari mutum bai isa ya fito kare na biye dashi ba,bare har ya dauki makami yana yawo dashi yana ihu,kuma kowa ya tashi kunnensa yana kan rediyo sauraren sabuwar doka kar yaje ya keta doka bai sani ba yasan ko waye shi hukunci za'ai masa yanzu fa?

    ReplyDelete
  2. INNA LILLAHI WA INNA ILAIHI RAAJI'OON!!!

    ReplyDelete
  3. Allah ya kyauta, rai ya zama kamar ran kiyashi?

    ReplyDelete
  4. Allah ka samar da zama Lafiya a wannan kasa tamu da duniya baki daya.

    ReplyDelete