Friday, 4 February 2011

Zanga-Zangar Masar: Ashe Mulki a Hannun Talakawa Ya Ke?


Yau a shirin BBC Hausa na Safe Nafisa Ahmed tayi wani rahoto wanda a cikinsa take tsokaci kan yadda karfin hadin kai tsakanin al'umma ke taka mahimmiyar rawa wajen juya akalar al’amuran siyasa a kasa. Nafisa tana bayani ne kan abubuwan da ke faruwa a wasu kasashen gabas ta tsakiya, amma musamman a Masar.

Jama’ar Masar sun yankewa kansu shawarar fitowa kan titinan babban birnin Alkahira da ma wasu biranen kasar, domin nuna kosawarsu da mulkin shugaba Hosni Mubarak, wanda ya shafe kusan shekaru 30 akan karagar mulki.

Jama’ar Masar sun jurewa mulkin Hosni Mubarak na tsahon wannan lokaci. Duk da haka kada a manta da rawar da tsohon sojen ya taka a harkokin mulki da tsaron kasar shekara da shekaru. Sai dai kuma a shekarun baya-bayan nan jama’a sun fara kaiwa magaryar tikewa da shugaba Mubarak.

Wannan kuwa na da nasaba da halin yanayin rayuwa a kasar ta Masar. Akwai matsaloli kamar talauci da rashin aikin yi musamman ma a tsakanin miliyoyin matasan kasar da kuma taka hakkin bil adama. Ga shi kuma uwa-uba ana zargin Mubarak yana shirin maida mulkin kasar na gado – wato ya nada dansa Gamal Mubarak a matsayin wanda zai gaje shi.

A takaice dai jama’ar Masar sun tsaya tsayin-daka ne, suna masu jajircewa mulkin danniya, zalunci da kuma yiwa tsarin democradiyya karen tsaye.

A karshe dai abunda ake hasashe zai faru a Masar din shine ra’ayin jama’a zai yi nasara akan ra’ayin mutum guda.

Yanzu haka saura kiris Hosni Mubarak ya zama tarihi a siyasar Masar. Sai dai abun takaici shine yadda bai yi hakan ba cikin daraja da mutunci; a’a sai da jama’ar kasar suka yi masa korar kare.

Wannan ba karamin darasi ne ba ga shugabannin kasashe, musammanma a kasashenmu, inda shugabani kan maida mulki tamkar kayan gado.

Abubuwan da suka faru a Masar da Tunisia da sauran kasashen Larabawa a ‘yan makonnin nan, sun nuna cewa ko shakka babu, iko ba a hannun shugabanni yake ba, a’a a hannun talakawan kasa yake.

Abunda ya kamata talakawan su yi kawai shine jajircewa, da rashin nuna gajiyawa, nuna rashin tsoro, kana da gujewa tashin hankali a yunkurinsu na kawo sauyi a kasarsu, domin kwatar ‘yancinsu da tabbatar da mulki na gari.

Hausuwa dai sun ce “gani ga wane, ya ishi wane tsoron Allah”. Allah ya tabbatar mana da mulki na adalci da rashin cin zali a kasashen mu, amin.

1 comment:

  1. kwarai da gaske hajia kinyi tsokaci na gamsarwa, yanda na karanta tsokacin nan wallahi sai naga cewa mu tamkar talakawan Najeriya kanmu a cikin duhu yake. ta yaya zamuyi ko da al'ummar Egyt da Tunisia? bacin zuciyarmu ta riga ta mutu da tsoro, ka bakin bindiga ma kadai ya ishi mu fargaba. Toh ga dai zabe ya taho muna dai fatan zamu chanja halayar mu a wannan karon ta sakawa kawunan mu ganye. Allah ya mana jagora. Aliyu M Umar Kwalli Kano

    ReplyDelete