Monday, 16 May 2011

Zaben 2011: Wancakalar da Babbar Dama


Zaben Nigeria na 2011 ya zo, ya tafi, ya kuma bar baya da kura. Babban makasudin wannan kura kuwa itace burin da jama’a suka dauka suka dorawa shugaban hukumar zaben da aka nada da zummar gudanar da zabuka masu inganci a kasar wato Farfesa Attahiru Jega, da kuma cewa a bana zasu yi amfani da kuri'arsu a matsayin babbar dama ta zabar wadanda zasu fish-she su daga halin la-haulan da suke ciki.

Kafin nada Jega 'yan Nigeria, da ma duniya gabakidaya, sun yi ittifakin cewa zabukan da aka yi a kasar a shekarun 2003 da 2007 ba wani abu bane, illa bankaura. Masu sa idanu kan wadancen zabukan sun bayyana cewa sune mafi muni a tarihin jefa kuri’a a Nigeria. Masu fafutukar wanzar da democradiyya a ciki da waje sun ta kokawar ganin an sauya tsarin zabe a Nigeria ta yadda zasu kasance ingantattu. Shi kansa shugaban da aka ce shi ya lashe zaben na 2007, marigayi Umaru Musa Yar’adua ya amince kan cewa lallai akwai bukatar yin gyara.

Saboda haka, bayan kasashen duniya musamman Amurka sun hurawa Nigeria wuta sai shugaba Goodluck Jonathan ya kawo Attahiru Jega a matsayin wanda zai gudanar da ingantattun zabuka a kasar. Sakamakon sunan da yayi a jami’a a matsayin “dan akida” da “taurin kai” sai jama’a suka ce, to zabe mai nagarta zai yiwu a Nigeria.

Sai dai tun sannan masu sharhi kan al’amuran siyasa a Nigeria kamar Dakta Junaidu Mohammed suka bayyana shakkunsu dangane da hakan. Suna masu cewa ai gyara ba zai yiwu idan mutun daya ne tak yake da manufar yin sa ba. Masu irin wannan ra’ayi sun dage kan cewa muddin dai ana san gyara, to wajibi ne Jega ya kori ma’aikatan hukumar zaben kasar INEC wadanda suka yi aiki a karkashin tsohon shugaban hukumar wanda ake yiwa kallon mazambaci wato Farfesa Maurice Iwu. Hakan dai bai faru ba.

A karshe dai ‘yan Nigeria sun kama hanyar jefa kuri’a ranar asabar 2 ga Afrilu, amma sai me? Ana tofa bisimillah, sai kwatsam, aka ba da sanarwar an dage zaben zuwa mako na gaba. Tun daga sannan ne gwiwowin jama’a da dama suka yi sanyi. A dan wannan lokaci an yi zargin kama manyan motoci makare da takardun zabe, da cewa sun yi sama ko kasa. Haka kuma jam’ian tsaro suma sun ta yin kalamai da suka ci karo da juna wadanda tun daga sannan jama’a suka ce, an ya kuwa?

Allah cikin ikonsa an yi zaben a haka – cikin zarge-zarge da fargaba, da tashe-tashen hankali, da abubuwan da ba zasu fadu ba.

Sai dai babban abunda ya fito wanda kuma shine babban abun takaici a wannan zaben shine yadda aka yi amfani da kudi, da kayan masarufi kamar sabulun wanka da shinkafa da taliyar Indomie, kiri-kiri a bainar jama’a, ba kunya, ba tsoro, dan jan hankalin masu zabe su zabi jam’iyyar da ke rabon kudin da kayan masarufin.

Abun bakin ciki shine, talauci da mutuwar zuciya sun yi tasiri, inda jama’a suka sa kafa suka shure damar da suke da ita ta kawo sauyi. A karshe sun zabi wadanda suka basu kudin da zai biya masu bukatar ‘yan kwanaki kilalan, a madadin wadanda ake ganin zasu kawo gyara na zahiri a kasa.

Wannan gajeren tunani ne a bangaren talakawa. Ba su tuna cewa wadanda suka basu kudin nan ba sune wadanda suka sa kafa suka dannan su cikin kuncin da suke ciki. Ba su tuna cewa kudin nan da aka dauko aka sammu su, dama nasu ne ba, wanda kuma da sune ya kamata a samar musu da wuta da ruwa da asibi da makarantu, amma aka ki yin hakan, sai da zabe yazo aka dan guzutso aka basu domin su mayar da yawu.

To a karshe talakawan Nigeria, da taimakon wadanda suka jefa su cikin kangin wahalar da suke ciki, sun wancakalar da damar da suka samu a 2011. Abunda yayi saura shine ko wadanda suka zaba a bana zasu fitar dasu daga matsanancin halin rayuwar da suke ciki ko a’a?

Da yace an ce Allah ya na baiwa al’umma shugabanni irin jama’arta, fatan mu kawai yanzu shine Ubangiji, Allah ya cece mu, Ya kawo mana sauyi tun daga cikin zukatanmu, mu kanmu, wanda kuma a karshe shi zai kaimu ga samun adalan shugabanni da zasu ciyar da kasar mu gaba.

Tuesday, 5 April 2011

Kancal A Shirin Zaben Nigeria


Zaben Nigeria na ci gaba da jan hankali a ciki da wajen kasar saboda dalilai da yawa. Kuma yanzu, fiye da kowanne lokaci, na yi imanin cewa duk kokarin mutum na kawo gyara a kasarmu, sai wasu sun yi kokarin kawo cikas, ko yin kancal!

Kowa dai ya san Profesa Attahiru Jega shugaban hukumar zaben Nigeria wato INEC, mutum ne mai akida. Kuma idan ya dage kan abu, ba’a iya tankwara shi.

Allah dai ya kai shi INEC, kuma tun sannan wasu suke cewa mai yiwuwa saboda akidarsa a samu ingantattun zabuka a Nigeria. Sai dai kuma wasu na cewa shi kadai ba zai iya kawo gyara ba. Inda masu musun farko ke cewa ai shugabanci na iya sauya na kasa. Ni ma ina daga cikin wadanda suka yi wannan fata.

Sai dai yayinda ni da sauran abokan aikina a BBC muka shirya kawowa ‘yan Nigeria rahotannin zaben da aka shirya yi a 2 ga watan Afrilu, sai kwatsam rahotannin matsaloli. A karshe dai an dage zabukan.

Dage zabukan sakamakon cikas din da aka samu abu ne da ya girgiza mutane da yawa. Sai dai mafi yawan ‘yan Nigeria na ci gaba da baiwa Jega goyon baya, suna masu cewa muddin dai zabukan zasu kasance na fisabilillahi, to ai dage su ba wani ba ne.

Ana dai ta hasashe da zarge-zarge cewa akwai wasu da suka hadiyi layer cewa zabukan nan ba zasu yi nasara ba ko ta halin hakaka saboda dalilan san-kai ba na san kasa ba. Idan haka ne Allah ya yi maganinsu domin bayin Allah.

A karshe ya zaman wajibi jam’ar Nigeria su jajirce wajen tabbatar adalci da samun shugabanni na gari.

Friday, 11 February 2011

Juyin-Juya Hali a Masar: Talakawa Sun Yi Nasara


Shi kenan ta faru ta kare. An kafa tarihi a Masar. Jama’ar kasar ta Masar sun yi nasarar kifar da gwamnatin shugaba Hosni Mubarak, mutumin da ya shafe shekaru 30 ynla wadaka da kasar Masar din.

Tsagwaron juriya da dagewa da tirjewa da kuma tsabagen hadin-kai sun tattara miliyoyin jama’a a sassan kasar daban-daban dan nuna cewa sun kai karshen lamba, dangane da lamuntar kama-karyar da shugaba Mubarak yake yi masu. ‘Yan Masar sun shafe kwanaki gome takwas suna kwana bisa titi, suna cewa lokacin Mubarak ya kare…Allah raka taki gona!

Abubuwa da yawa sun taimaka wajen cimma wannan buri na Misirawa. Baya ga dagewar jama’ar, da akwai juriya da hakuri da shan wahala… amma uwa-uba shine sadaukar da kai. Da yawa daga cikin jama’ar Masar din sun san cewa mai yiwuwa rikicin ya ritsa da su – ma’ana, mai yiwuwa su rasa rayukansa. Wannan, bai hana su tsaya kan bakan su ba. Kuma a zahiri daruruwan sun hallaka din.

Wani abu kuma da ya fito fili shine fusahar zamani ta taimaka wajen tattaro masu irin wannan buri. Miliyoyin jama’a sun ta amfani da na’urar internet da wayoyin salula wajen yada manufofinsu, kana suka yi ta amfani da dandalin muhawara da musanyar bayanai na facebook da twitter da sauransu, wajen fadada kamfe din su.

A karshe dai kamfe din nasu ya mamaye kusan manyan biranen kasar, inda a kwanakin baya-bayan nan kungiyoyin ma’aikata su ma, suka shiga yajin aiki na sai-illa-masha-Allahu. Hakan ya karawa masu zanga-zangar kaimi, inda suka gano cewa, suna kara samun goyon baya daga jama’ar Masar din.

A karshe dai abunda ya faru a Masar juyin-juya hali ne mai matsanancin tarihi; wanda kuma zai yi tasiri a duk fadin duniya.

Babban sakon juyin juya halin Masar shine: KAN MAGE YA WAYE!

Mulki a hannun jama’a yake, ba’a hannun shugababanni ba. Ko shakka babu, wasu shugabannin da suka maida mulki tamkar kayan gado, zasu fuskanci makoma irin ta Hosni Mubarak.

Bari mu zura idanu mu ga wacce kasa ce zata biyo bayan Masar dangane da sabuwar iskar juyin juya halin da yanzu haka take kadawa a duniya!

Allah ya baiwa talakawa sa’a amin!

Friday, 4 February 2011

Zanga-Zangar Masar: Ashe Mulki a Hannun Talakawa Ya Ke?


Yau a shirin BBC Hausa na Safe Nafisa Ahmed tayi wani rahoto wanda a cikinsa take tsokaci kan yadda karfin hadin kai tsakanin al'umma ke taka mahimmiyar rawa wajen juya akalar al’amuran siyasa a kasa. Nafisa tana bayani ne kan abubuwan da ke faruwa a wasu kasashen gabas ta tsakiya, amma musamman a Masar.

Jama’ar Masar sun yankewa kansu shawarar fitowa kan titinan babban birnin Alkahira da ma wasu biranen kasar, domin nuna kosawarsu da mulkin shugaba Hosni Mubarak, wanda ya shafe kusan shekaru 30 akan karagar mulki.

Jama’ar Masar sun jurewa mulkin Hosni Mubarak na tsahon wannan lokaci. Duk da haka kada a manta da rawar da tsohon sojen ya taka a harkokin mulki da tsaron kasar shekara da shekaru. Sai dai kuma a shekarun baya-bayan nan jama’a sun fara kaiwa magaryar tikewa da shugaba Mubarak.

Wannan kuwa na da nasaba da halin yanayin rayuwa a kasar ta Masar. Akwai matsaloli kamar talauci da rashin aikin yi musamman ma a tsakanin miliyoyin matasan kasar da kuma taka hakkin bil adama. Ga shi kuma uwa-uba ana zargin Mubarak yana shirin maida mulkin kasar na gado – wato ya nada dansa Gamal Mubarak a matsayin wanda zai gaje shi.

A takaice dai jama’ar Masar sun tsaya tsayin-daka ne, suna masu jajircewa mulkin danniya, zalunci da kuma yiwa tsarin democradiyya karen tsaye.

A karshe dai abunda ake hasashe zai faru a Masar din shine ra’ayin jama’a zai yi nasara akan ra’ayin mutum guda.

Yanzu haka saura kiris Hosni Mubarak ya zama tarihi a siyasar Masar. Sai dai abun takaici shine yadda bai yi hakan ba cikin daraja da mutunci; a’a sai da jama’ar kasar suka yi masa korar kare.

Wannan ba karamin darasi ne ba ga shugabannin kasashe, musammanma a kasashenmu, inda shugabani kan maida mulki tamkar kayan gado.

Abubuwan da suka faru a Masar da Tunisia da sauran kasashen Larabawa a ‘yan makonnin nan, sun nuna cewa ko shakka babu, iko ba a hannun shugabanni yake ba, a’a a hannun talakawan kasa yake.

Abunda ya kamata talakawan su yi kawai shine jajircewa, da rashin nuna gajiyawa, nuna rashin tsoro, kana da gujewa tashin hankali a yunkurinsu na kawo sauyi a kasarsu, domin kwatar ‘yancinsu da tabbatar da mulki na gari.

Hausuwa dai sun ce “gani ga wane, ya ishi wane tsoron Allah”. Allah ya tabbatar mana da mulki na adalci da rashin cin zali a kasashen mu, amin.

Tuesday, 4 January 2011

Mun Shigo 2011 da Tashin Bama-Bamai a Nigeria


Bam ya tashi a Jos! Wannan shine sakon da Bashir Saad Abdullahi ya aiko mani ranar 24 ga watan Disambar 2010.

Wannan harin bam ya tashi ne a wata majami’a ana jaji berin Kirsimeti. Kuma bayan harim bam din na Jos sai aka ci gaba da samun wasu hare-hare ciki harda a Bayelsa da birnin tarayya, Abuja – wato cibiyar gwamnatin Nigeriar.

An dai samu hasarar rayuka da jikkata bayin Allah a wadannan hare-hare. Hare-haren na nuni da mummunan halin rashin tsaron da aka shiga a Nigeria. Gashi kuma lamarin na faruwa a daidai lokaci da kasar ke shirin gudanar da zabuka a duk fadinta a watan Afrilun nan mai zuwa.

Rashin tsaron Nigeria ya samo asali ne sakamakon yin biris da ake zargin jami’an tsaro da shugannin kasa suke yi da harkokin tsaro. Haka kuma ana zargin wasu matsalolin da suka hada da rashin sanin makamar aiki, da san kai a madadin san kasa da kuma tsohuwar matsalar nan dake addabar Nigeria wato cin hanci.

Ko ma dai menene, abunda fashewar bama-baman na makon jiya ke nuni da su shine, Nigeria ta shiga wani sabon babi a fannin rashin tsaro a kasar. Kuma abunda ke faruwa zai kara tsanani muddin dai shugabannin siyasa basu fito sun gudanar da bincike na fisa-bilillahi, kana suka hukunta duk wanda ke da hannu a haddasa tashe-tashen hankula a kasar ba – kana su yi hakan ba sani ba sabo. Muddin ba’a yi haka ba, to za’a yi ta surutu ne ba tare da magance matsalar ba.

Wajibi kuma jama’a su kwarmata duk wani yunkuri da suka ji ana yi na kokarin haddasa masifa a yankunansu. Su tuna cewa: ai idan bam bai fada akanka ba, to idan ya fada kan mahaifinka, ko dan-uwanka tamkar ta fada a kanka ne.

A karshe sai mu ci gaba da yiwa kasar mu addu’ar zaman lafiya da kwanciyar hankali domin samun ci gaba.

Thursday, 23 December 2010

Shugabannin Afrika Na Karen Tsaye ga Democradiyya


Zabuka a nahiyar Afrika na neman zama wani abu daban. Abubuwan da yanzu haka ke faruwa a kasar Cote d’Ivoire abubuwa ne da ke tayar da hankali ga duk wani mai san ganin ci gaba a nahiyar Afrika, abubuwa ne dake tayar da hankali ga ma’abota tsarin mulki irin na democradiyya.

Bayan shafe shekaru 10 yana mulki a kasar ta yammacin Afrika, da kyar da jibin goshi Laurent Gabgbo ya amince ya gudanar da zaben kasa baki daya. Dama dai kada mu manta cewa kasar ta yi fama da yaki da tashe-tashen hankula, lamarin da sai da kasashen duniya da majalisar dinkin duniya suka yi wurjanjan kafin su kawo karshen sa.

A watan jiya an yi zabe. Kuma ‘yar manuniya ta nuna. Abunda kuwa ta nuna shine cewa Alhassan Ouattara ne ya lashe zaben. Amma sai me zai faru?

Sai shugaban da ya shirya zaben Laurent Gabgbo yayi kememe ya ce ba zai sauka daga mukami ba, bayan kuwa hukumar zaben kasar mai zaman kanta ta bayyana sakamakon da ya nuna Alhassan Ouattara ne ya yi nasara.

Laurent Gabgbo ya rantsar da kansa a matsayin zababben shugaban kasa. Shima kuma Alhassan Ouattara ya bayyana kansa a matsayin sabon shugaban kasar ta Cote d’Ivoire.

Kasashen duniya sun yi Allah wadai da karan-tsayen na Mr Gagbo, kuma kawo yanzu tuni har an fara zub da jini, abunda kuma Allah kadai ne ya san inda lamarin zai tsaya.

Babban abunda lamarin na Cote d’Ivoire ke nunawa shine shugabannin Afrika basu san menene democradiyay ba. Basu yadda cewa jama’a zasu iya sauya shugabanninsu ta hanyar dangwala dan-yatsa bisa katin zabe ba.

Yana kuma nuna cewa shugabannin Afrika ‘yan kama-karya ne, wadanda ba sa mutunta bukatun jama’arsu. Dama a ce ma suna yiwa kasa aiki ne, suna kawo kyakkyawan ci gaba ga rayuwar talakawa, to dama da sauki. To amma mulki a nahiyar abune na “ramin-kura”.

Kada kowa ya raba daya biyu cewa abunda ya faru a Cote d’Ivoire ba zai iya faruwa a sauran kasashen Afrika ba. Ko shakka babu hakan zai iya faruwa a kowacce kasa a nahiyar; domin kuwa launin shugabannin – abunda Hausawa ke cewa ne – duka kanwar ja ce.

Sai dai manyan tambayoyi su ne: har ya zuwa yaushe ne jama’ar Afrika, da talakawa zasu ci gaba da amincewa da mulkin kama-karya? Har zuwa yaushe ne shugabanni za su ci gaba da taka bayin Allah saboda suna takama da karfin iko da kujerar da suke kai?

Mai yiwuwa talaka ba zai iya ba, kodai saboda tsoro, ko saboda rashin sanin ‘yancin kansa. Sai dai idan su ba zasu iya ba, Allah zai iya musu.

A karshe ina mai tsinkayen wani lokaci a gaba, da idan ance shugaba yayi irin abunda ke wakana a Cote d’Ivoire yanzu, zai ranta a na kare, ya ce “ku rufa mani asiri”.

Allah ya nuna mana wannan lokaci ko mulkin adalci da gaskiya ya wanzu a nahiyar mu. Allah ya kawo mana karshen karen-tsayen da shugabanni ke yiwa tsarin democradiyya a Afrika.