Wednesday, 28 April 2010

Matasa da Bangar Siyasa a Nigeria


Yanzu haka an fara shiga yanayin siyasa a Nigeria wato yayinda ake shirin gudanar da zabukan shekara mai zuwa.

Siyasa na da mahimmanci a kowacce kasa ta duniya dake bin tarafkin democradiyya. Dalili kuwa shine siyasar tsarin democradiyya na baiwa jama’a damar zabar wanda suke ganin ya dace da su, kuma wanda zai biya masu bukatun su da kuma share masu hawaye.

Jama’a kan ba da goyon baya ga wanda suka yi imanin zai wakilce su – kuma wakilci na gari – ba wanda zai je dan wakiltar kan sa ba. Ta yaya jama’a ya kamata su tabbatar da cewa sun zabi na gari ba zaben tumun dare ba?

Mai yiwuwa sai nan gaba zamu tattauna wannan batu. Amma ina so na yi a wannan sharhi ne akan siyasar banga.

Tun bayan da Nigeria ta koma tsarin democradiyya yau shekaru sama da goma ‘yan siyasar kasar ke amfani da matasa domin cimma manufofin su na siyasa. Ba laifi ba ne ‘yan siyasa su nemi goyon bayan matasa. Misali a baya-bayan nan, kuri’a da goyon bayan matasan Amruka ta taimaka gaya wajen nasarar shugaba Barack Obama a 2008.

Abunda yake laifi shine amfani da matasa a matsayin ‘yan bangar siyasa domin samun nasara a zabe. A zabukan da suka wakana a baya ‘yan siyasa a Nigeria na baiwa matasa kudi, inda su kuma sukan sayi kwaya da sauran ababen sa maye da makamai, suna bi suna razana abokan hamayya da sauran jama’a.

Kamar yadda na gani a wannan hoto dake kan wannan shafi (wanda na dauka sa’ilin da na kai ziyara Bauci a watan jiya), rikici kan rincabe tsakanin ‘yan bangar siyasa. Akan yi fito-na-fito tsakanin ‘yan bangar ‘yan siyasar. Wani lokaci a ji munanan raunuka, a wasu lokuta a rasa rayuka. Wannan abun takaici ne.

Shin matasan nan da suke bari ana amfani da su dan cimma manufar zabe, duk da cewa sun san ‘yan siyasa zasu yi watsi da su, da zarar sun yi nasara, sun san ciwon kan su kuwa? Suna da masaniya kan cewa ‘yan siyasa basu damu da su ba illa kawai sun mai da su tamkar matattakala ce da suke takawa domin “cin zabe” ko ta halin kaka?

Amsar da nake san sani itace: ta yaya ne matasa zasu jajirce su ki yarda ana amfani da su a matsayin ‘yan bangar siyasa a bisa kudi kalilan – wadanda akewa kallon marasa mutunci a Nigeria - lamarin da ka iya sanadiyyar hasarar rayukan su da ci bayan kasar su?

5 comments:

  1. Lalle kam Hajia maganarki dutse. Ina ganin babban abinda matasa ke sa su shiga wadan nan lamura basa wuce: Talauci da ganda, tare da mutuwar zuci, da kuma rashin ciwan kansu. Muddum idan muka tashi tsaye wajen kam sana o'i toh ba ta yandda yan siyasa zasu ruka amfani damu dan cimma burinsu, bujirewa karbar kudadan yan siyasa a wannan lokaci abu ne mai matukar wuya domin sun ruga sun mamaye zuciyar su a haka (kamar yadda nace din ne, matasa sai sun yaki zuciyar su a nan).
    Ta bangaran iyaye ma suma nada nasu gudummawar wajen baiwa matasan izinin shiga bangar siyasa "domin itace hanyar da zata fitar dasu daga talaucin da suke fama da shi" amma ace warsu.
    Yanzu haka a jihar dana fito wato, jihar Kano ana yiwa wadannan matasan lakabi da YAN JAGALIYA! Ana zan iya cewa mutuwar zuci ce ta kawo haka. Ya kamata yan uwana matasa duk abubuwan da suka faru a baya su zamar mana darasi mana, dafatan zamu chanja a zaben 2011 Allah kasa matasa mu gane hanyar gaskiya. Aliyu Mukhtar Umar Kwalli Kano

    ReplyDelete
  2. Hajia wannan wata matsala datafi kamari a Arewacin najeriya kuma aba ce wacce idan ba ni dake da Gwamnati da kuma uwa-uba iyaye ba ba za'a taba kauda shi a kasar mu Najeriya ba.
    dalilai na kuwa sune:
    1. Yaki da talauci na gaskiya
    2. Ilmi na kwarai
    3. tarbiya ta kwarai

    Idan ba an yaki jahilci cikin matasa ba to ba yadda zasu gane yan'cin su har kuma su tsare shi
    Wannan kuwa yana bukatar ilmi na kwarai wnda zaisa su fahimci rayuwa a addinance da kuma rayuwa ingantacciya ta duniya.
    Ama uwa uba dole ne iyaye su bada tarbiyya ta kwarai wa yaransu ta yadda zasu gane wanene mai gaskiya kuma wanene azzalumi ko mayaudari don su guje masa.Kuma susan cewa idan tafiya za'ayi ko wace iri ce, akwai ya'yan dan wannan siyasar cikin tafiyar ko basu? idan tafiya ta halaka ce basu sa ya'yansu ciki sai dai ya'yan talakawa.
    Idan har zamu iya tsare wannan ka'idojin to lallai za'a rage bangar siyasa kwarai da gaske. Daga Abbas G Idriss, Kaduna Najeriya +234 803 303 6069

    ReplyDelete
  3. @Sakali, maganar ka da kamshin gaskiya, sai dai ta wani bangare guda me yasa matasan kudancin Najeria yawancin basu fiya shiga bangar siyasa ba? Kamar yadda mu tayi kamari a nan arewa, shin ko namu shuwaga bannin ne basu da kishin mu?. Ba ta yadda za'a yaki talauci sai mu al'umma mun yaki zuciyarmu daga hangen abinda bashi da tabbas, ice tun yana karami ake tankwasa shi, a nan ina gani lokaci ya kurewa iyaye sai dai ayi toshe daga farko.

    ReplyDelete
  4. To Amma Aliyu da Sakali...ta yaya ku da kanku matasa zaku taimaka wajen magance wannan matsalar?

    ReplyDelete
  5. Assalm. Hajia sai yau Allah ya nufeni da ganin comment dinki.
    Hajia, kamar yadda nace ne a baya, tushen farko sai mu matasa mun hada kawunan mu guri daya, kuma mun tashi tsaye mun cire ganda da kama sana'o'i.
    Zaiyi wuya a dan wannan lokaci a iya shawo kan masu irin wannan dabi'ar domin lokaci ya kure mana amma a ganina, don tuni matasan suka busa algaitar su da kulla damarar shiga hidumin siyasar. Sai dai idan muka bude kungiyoyin taimakwan juna zamu iya samun cigaba, kamar dai yadda muka fara a unguwar mu ta kwalli don har ire iren matasan sun fara karbar ilimin islama haka kuma zamuyi kokarin habaka ta. Allah dai ya mana jagora amin.

    ReplyDelete