Wednesday, 23 June 2010

Dambe a Majalisar Nigeria: Halin Dattaku?



Hoton dan majalisar wakilan Nigeria kenan Dino Melaye, shugaban kwamitin “Progressive Forum” masu fafutukar kawo sauyi a majalisar wakilan Nigeria. Hotan na nuni da yadda taguwar da yake sanye da ita, ta yage, kana gashi yana sharba gumi. An dai dauki hoton wannan dan majalisar ne bayan damben da aka sha a majalisar wakilan Nigeriar.

Majalisa ta nemi a fitar da ‘yan kungiyar “Progressives” din ne da karfin tuwo bayan sun nemi da a binciki shugaban majalisar wakilan Dimeji Bankole a bisa zargin sama da fadi da kudin jama’a da mulkin kama-karya. Wasu ‘yan majalisar sun fito shabe-shabe yayinda shi kuwa dan majalisa Chinyere Igwe ya samu karaya a hannu bayan wani dan majalisar ya kai masa hari da tukunyar iskar kashe gobara.

Rikici a majalisar dai ya barke ne a jiya (22/06/10) bayan da jim kadan bayan majalisar ta fara zaman ta, kakakinta Bankole ya nemi wani dan majalisa da ya gabatar da moshan (kuduri).

Amma da Mr Melaye ya dago cewa ana kokarin gabatar da moshan din da zai dakatar da ‘yan Progressives” din daga majalisa, sai ya mike, ya fara ihu, yana cewa, “ babu hali, babu hali, ba zamu yadda ba”, yana kuma busa wani usur da ya shiga da shi cikin majalisar.

Kafin a ankara sai wuri ya yamutse, sai naushin juna. An dai yi wannan lamarin ne a gaban ‘yan jarida wadanda kuma suka dauki hotuna da bidiyo. Nan take kuma wasu ‘yan majalisar da jami’an tsaro suka yi kokarin kwace hotunan da ‘yan jarida suka dauka saboda kada duniya ta ga abun kunyar da shugabannin jama’ar suka aikata.

Tuni dai jama’a a ciki da wajen Nigeria suke ta bayyana ra’ayinsu dangane da halayyar mutanen da aka dorawa alhakin yin doka a Nigeria.

A tsakanin kowacce al’umma dake da nutsuwa da sanin ya kamata dai akwai wasu halayya da dabi’u da ya kamata manya su nuna. Mutunta juna, musamman wajen tunkarar mai da martani ga ra’ayin da ya banbanta da na wani na ga kan gaba.

Tsarin democradiyya kuma na jaddada mahimmancin muhawara da bayyana ra’ayi, amma cikin hankali da kwanciyar hankali ba ta hanyar zagi-in-zaga da doke-doke ba.

Dambe da baiwa hammata iska da amfani da makami dan jikkata wani, baya daga cikin halayya ko dabi’un da ake alakantawa da zababbun wakilai masu yiwa kasa doka. Idan kuwa suka yi hakan, lamarin ya kasance mai dokar barci ya bige da gyangyadi kenan. Kuma wabiji ne a hukunta su domin hana faruwar hakan a gaba. Babba, ai misali mai kyau ya kamata ya nunawa na kasa!

Masu sharhi na cewa damben da ya faru a majalisar wakilan Nigeria abun takaici ne. Kuma a cewar su, na nuni da rashin sanin ya kamata da karya mutuncin tsarin democradiyya a Nigeria. Wasu suka ce a daidai wannan lokaci da Nigeria ke kokarin gyara martabar ta a idanun duniya “re-branding”, sai ga manyan jami’an tsarin democradiyya kasar suna kokawa da juna. Tuni dai hotunan wannan abun kunya suka mamaye yanar gizo “internet” inda miliyoyin jama’a suke ta dubawa suna sharhi.

Daga cikin tambayoyin da ake yi yanzu haka har da: shin ‘yan majalisar Nigeriar suna dambe da juna ne saboda kare hakkokin jama’ar da suke wakilta, wadanda kuma talauci da matsayin rayuwa ya addaba, ko kuwa suna baiwa hammata iske ne bisa wasu bukatu na su na kashin kansu?

Sashen Hausa na BBC zai duba wannan batu a wannan makon a shirin sa na “Ra’ayi Riga”.

2 comments:

  1. Wallahi Haj. Jamila, wannan ba karamin abun kunya bane tunda har masu dokar barci zasu buge da gyangyadi.

    Ya kamata matasan da talakawan Nigeria mu tashi tsaye don ganin mun zabi wadanda suka can-canta su wakilce mu a kowanne irin shigabanci ne, ba wadanda zasu bamu kudiba suje suna ta shirme da son kansu kadai.

    Allah Ya shirya mana, ameen.

    ReplyDelete
  2. Hajia ina fa wannan halin yara ne yan Primary. Abin kunya da Allah wadai Suna wakilan al'umma amma su ke da irin wannan hali kuma idan akayi bincike mai zurfi za'a ga cewa, duk sunayin wannan dabi'ar ne domin bukatun kansu, yawancin su basu san mene aikin majalisa sai dumama kujera.
    Kawai wannan ya rage namu, darasi ne zamu karanta musan wayanda zasu rika wakiltar mu ba SHAGON Arewa ko na kudu ba. Allah yasa mu talakawa mu chanja bara gurbi a zaben 2011. Allah ya mana jagora, amin

    ReplyDelete