Matattarar ra'ayi, da tunani kan al'ummaran yankin Arewa, da Nigeria da sauran sassan duniya.
Monday, 16 May 2011
Zaben 2011: Wancakalar da Babbar Dama
Zaben Nigeria na 2011 ya zo, ya tafi, ya kuma bar baya da kura. Babban makasudin wannan kura kuwa itace burin da jama’a suka dauka suka dorawa shugaban hukumar zaben da aka nada da zummar gudanar da zabuka masu inganci a kasar wato Farfesa Attahiru Jega, da kuma cewa a bana zasu yi amfani da kuri'arsu a matsayin babbar dama ta zabar wadanda zasu fish-she su daga halin la-haulan da suke ciki.
Kafin nada Jega 'yan Nigeria, da ma duniya gabakidaya, sun yi ittifakin cewa zabukan da aka yi a kasar a shekarun 2003 da 2007 ba wani abu bane, illa bankaura. Masu sa idanu kan wadancen zabukan sun bayyana cewa sune mafi muni a tarihin jefa kuri’a a Nigeria. Masu fafutukar wanzar da democradiyya a ciki da waje sun ta kokawar ganin an sauya tsarin zabe a Nigeria ta yadda zasu kasance ingantattu. Shi kansa shugaban da aka ce shi ya lashe zaben na 2007, marigayi Umaru Musa Yar’adua ya amince kan cewa lallai akwai bukatar yin gyara.
Saboda haka, bayan kasashen duniya musamman Amurka sun hurawa Nigeria wuta sai shugaba Goodluck Jonathan ya kawo Attahiru Jega a matsayin wanda zai gudanar da ingantattun zabuka a kasar. Sakamakon sunan da yayi a jami’a a matsayin “dan akida” da “taurin kai” sai jama’a suka ce, to zabe mai nagarta zai yiwu a Nigeria.
Sai dai tun sannan masu sharhi kan al’amuran siyasa a Nigeria kamar Dakta Junaidu Mohammed suka bayyana shakkunsu dangane da hakan. Suna masu cewa ai gyara ba zai yiwu idan mutun daya ne tak yake da manufar yin sa ba. Masu irin wannan ra’ayi sun dage kan cewa muddin dai ana san gyara, to wajibi ne Jega ya kori ma’aikatan hukumar zaben kasar INEC wadanda suka yi aiki a karkashin tsohon shugaban hukumar wanda ake yiwa kallon mazambaci wato Farfesa Maurice Iwu. Hakan dai bai faru ba.
A karshe dai ‘yan Nigeria sun kama hanyar jefa kuri’a ranar asabar 2 ga Afrilu, amma sai me? Ana tofa bisimillah, sai kwatsam, aka ba da sanarwar an dage zaben zuwa mako na gaba. Tun daga sannan ne gwiwowin jama’a da dama suka yi sanyi. A dan wannan lokaci an yi zargin kama manyan motoci makare da takardun zabe, da cewa sun yi sama ko kasa. Haka kuma jam’ian tsaro suma sun ta yin kalamai da suka ci karo da juna wadanda tun daga sannan jama’a suka ce, an ya kuwa?
Allah cikin ikonsa an yi zaben a haka – cikin zarge-zarge da fargaba, da tashe-tashen hankali, da abubuwan da ba zasu fadu ba.
Sai dai babban abunda ya fito wanda kuma shine babban abun takaici a wannan zaben shine yadda aka yi amfani da kudi, da kayan masarufi kamar sabulun wanka da shinkafa da taliyar Indomie, kiri-kiri a bainar jama’a, ba kunya, ba tsoro, dan jan hankalin masu zabe su zabi jam’iyyar da ke rabon kudin da kayan masarufin.
Abun bakin ciki shine, talauci da mutuwar zuciya sun yi tasiri, inda jama’a suka sa kafa suka shure damar da suke da ita ta kawo sauyi. A karshe sun zabi wadanda suka basu kudin da zai biya masu bukatar ‘yan kwanaki kilalan, a madadin wadanda ake ganin zasu kawo gyara na zahiri a kasa.
Wannan gajeren tunani ne a bangaren talakawa. Ba su tuna cewa wadanda suka basu kudin nan ba sune wadanda suka sa kafa suka dannan su cikin kuncin da suke ciki. Ba su tuna cewa kudin nan da aka dauko aka sammu su, dama nasu ne ba, wanda kuma da sune ya kamata a samar musu da wuta da ruwa da asibi da makarantu, amma aka ki yin hakan, sai da zabe yazo aka dan guzutso aka basu domin su mayar da yawu.
To a karshe talakawan Nigeria, da taimakon wadanda suka jefa su cikin kangin wahalar da suke ciki, sun wancakalar da damar da suka samu a 2011. Abunda yayi saura shine ko wadanda suka zaba a bana zasu fitar dasu daga matsanancin halin rayuwar da suke ciki ko a’a?
Da yace an ce Allah ya na baiwa al’umma shugabanni irin jama’arta, fatan mu kawai yanzu shine Ubangiji, Allah ya cece mu, Ya kawo mana sauyi tun daga cikin zukatanmu, mu kanmu, wanda kuma a karshe shi zai kaimu ga samun adalan shugabanni da zasu ciyar da kasar mu gaba.
Subscribe to:
Posts (Atom)