Tuesday 29 June 2010

Talauci na Janyo Mutuwar Mata Wajen Haihuwa


Da alama matsalar mutuwar mata sanadiyyar haihuwa, na ci gaba da ci wa al'ummar yankin arewacin Nigeria tuwo a kwarya. Kodayake dai wannan ba matsala ce da ta addabi kasar Nigeria kawai ba, a'a sauran kasashe masu tasowa musamman ma a nahiyar Africa su ma suna dimbin hasarar rayukan mata da jira-jirai. Alkaluman hukumar UNICEF na nuna mace daya daga cikin goma sha-uku na mata masu juna biyu kan rasa rayukan su a lokacin haihuwa a nahiyar Afrika.

A wani rahoton BBC, wakilin jihar Jigawa, Muhammad Annur Muhammad, ya bayyana cewa a shekaru ukun da suka shige, alkaluma sun nuna cewa jihar Jigawan ce kan gaba a Nigeria a wannan matsala.

A jihar Borno ma, mata na rasa rayukan su a kullum idan suka zo haihuwa. Duk da bayanan da suke nuna cewa an soma samun nasarar rage matsalar a wasu kasashen tun bayan rattaba hannun kan kudurorin Muradan Majalisar Dinkin Duniya na shekara ta 2015 da shuwagabannin kasashe 147 suka yi, har yanzu akwai jan aiki a gaban Bornon. Lamarin haka yake ma a sauran jihohin arewacin Nigeria. Kodayake dai an tabbatar da cewa shiyyar arewa maso gabashin Najeriyar ce da har yanzu alkaluma ke nuna matsalar tafi ta'azzara.

Amma kuma wasu jihohin arewacin Nigeriar na dan tabusawa. A jihar Jigawa, Mohammed Annur Mohammed na BBC Hausa, ya ce gwamnatin jihar ta shigo da wani shiri wanda ya kunshi horar da al'ummomi musamman na yankunan karkara su kafa wata kungiya da hukumomin ke ilmantar da su bisa hanyoyin kula da mata masu juna biyu, tare da ba su motoci don hanzarta kai matan asibiti.

Akwai matsaloli daban-daban dake janyo mutuwar mata masu juna biyu idan suka zo haihuwa. Babbar matsala dai ita ce talauci. Matan talakawa masu juna biyu sun fi yiwuwar mutuwa idan aka kwatanta da matan mazaje masu hannu da shuni. Saboda rashi, matan talakawa ba sa samun abinci mai gina jiki.

Baya ga wannan, sukan yi ayyuka na karfi, da wahala kamar su noma da surfe da sussuka, har zuwa lokacin da suke gab da zuwa kan-gwiwa. Karfin su kan kare a lokacin da haihuwar ta zo, wanda kuma a lokacin ne suka fi bukatar karfin.

Haka kuma mata marasa ilimi sun fi yiwuwar rasuwa wajen haihuwa fiye da mata masu ilimi saboda sun fi su sanin hanyoyin kaucewa daga wasu haddura; kana sun fi su sanin mahimmancin zuwa asibiti - tun daga lokacin awan ciki har ya zuwa lokacin haihuwa. Alal misali kididdiga ta nuna mata masu ciki biyu cikin goma ne kawai ke zuwa asibiti a jihar Jigawa a yayin da suke da juna biyu.

Matan dake zaune a kauyuka sun fi yiwuwar rasuwa a wajen haihuwa fiye da matan dake zaune a birane. Rashin asibitoci a kauyuka ko kuma nisan da suka yi daga birane na nufin mata masu juna biyu basu cika samun kulawa cikin hanzari a lokacin da suke nakuda ba. So tari kan a je asibiti, sai ka ga rai yayi halin sa. So tari ma har da na jaririn.

Muddin dai yankin Arewacin Nigeria na san cimma manufofin raya kasa, bunkasa da tattalin al'ummar su, ya zama wajibi su tashi haikan wajen tabbatar da daukar matakan da zasu magance wannan matsalar dake janyo hasara mai dimbin yawa ga yankin. Saka idanu wajen kula da jama'a, musamman talakawa babban hakki ne da ya kamata su sauke.

Wednesday 23 June 2010

Dambe a Majalisar Nigeria: Halin Dattaku?



Hoton dan majalisar wakilan Nigeria kenan Dino Melaye, shugaban kwamitin “Progressive Forum” masu fafutukar kawo sauyi a majalisar wakilan Nigeria. Hotan na nuni da yadda taguwar da yake sanye da ita, ta yage, kana gashi yana sharba gumi. An dai dauki hoton wannan dan majalisar ne bayan damben da aka sha a majalisar wakilan Nigeriar.

Majalisa ta nemi a fitar da ‘yan kungiyar “Progressives” din ne da karfin tuwo bayan sun nemi da a binciki shugaban majalisar wakilan Dimeji Bankole a bisa zargin sama da fadi da kudin jama’a da mulkin kama-karya. Wasu ‘yan majalisar sun fito shabe-shabe yayinda shi kuwa dan majalisa Chinyere Igwe ya samu karaya a hannu bayan wani dan majalisar ya kai masa hari da tukunyar iskar kashe gobara.

Rikici a majalisar dai ya barke ne a jiya (22/06/10) bayan da jim kadan bayan majalisar ta fara zaman ta, kakakinta Bankole ya nemi wani dan majalisa da ya gabatar da moshan (kuduri).

Amma da Mr Melaye ya dago cewa ana kokarin gabatar da moshan din da zai dakatar da ‘yan Progressives” din daga majalisa, sai ya mike, ya fara ihu, yana cewa, “ babu hali, babu hali, ba zamu yadda ba”, yana kuma busa wani usur da ya shiga da shi cikin majalisar.

Kafin a ankara sai wuri ya yamutse, sai naushin juna. An dai yi wannan lamarin ne a gaban ‘yan jarida wadanda kuma suka dauki hotuna da bidiyo. Nan take kuma wasu ‘yan majalisar da jami’an tsaro suka yi kokarin kwace hotunan da ‘yan jarida suka dauka saboda kada duniya ta ga abun kunyar da shugabannin jama’ar suka aikata.

Tuni dai jama’a a ciki da wajen Nigeria suke ta bayyana ra’ayinsu dangane da halayyar mutanen da aka dorawa alhakin yin doka a Nigeria.

A tsakanin kowacce al’umma dake da nutsuwa da sanin ya kamata dai akwai wasu halayya da dabi’u da ya kamata manya su nuna. Mutunta juna, musamman wajen tunkarar mai da martani ga ra’ayin da ya banbanta da na wani na ga kan gaba.

Tsarin democradiyya kuma na jaddada mahimmancin muhawara da bayyana ra’ayi, amma cikin hankali da kwanciyar hankali ba ta hanyar zagi-in-zaga da doke-doke ba.

Dambe da baiwa hammata iska da amfani da makami dan jikkata wani, baya daga cikin halayya ko dabi’un da ake alakantawa da zababbun wakilai masu yiwa kasa doka. Idan kuwa suka yi hakan, lamarin ya kasance mai dokar barci ya bige da gyangyadi kenan. Kuma wabiji ne a hukunta su domin hana faruwar hakan a gaba. Babba, ai misali mai kyau ya kamata ya nunawa na kasa!

Masu sharhi na cewa damben da ya faru a majalisar wakilan Nigeria abun takaici ne. Kuma a cewar su, na nuni da rashin sanin ya kamata da karya mutuncin tsarin democradiyya a Nigeria. Wasu suka ce a daidai wannan lokaci da Nigeria ke kokarin gyara martabar ta a idanun duniya “re-branding”, sai ga manyan jami’an tsarin democradiyya kasar suna kokawa da juna. Tuni dai hotunan wannan abun kunya suka mamaye yanar gizo “internet” inda miliyoyin jama’a suke ta dubawa suna sharhi.

Daga cikin tambayoyin da ake yi yanzu haka har da: shin ‘yan majalisar Nigeriar suna dambe da juna ne saboda kare hakkokin jama’ar da suke wakilta, wadanda kuma talauci da matsayin rayuwa ya addaba, ko kuwa suna baiwa hammata iske ne bisa wasu bukatu na su na kashin kansu?

Sashen Hausa na BBC zai duba wannan batu a wannan makon a shirin sa na “Ra’ayi Riga”.