Sunday 28 February 2010

Kiwon Lafiya a Arewacin Nigeria


A shirin BBC Hausa na safiyar yau an yi wani labari da ya taba ni sosai. Labarin shine na wasu iyaye mata dake dawainiya da 'ya'yan su dake da cutar amosanin jini wato “sickle cell” a turance. Dan jaridar BBC Nura Mohammed Ringim yayi hira da wata mace Hajiya Ba'adiya Magaji wadda dan ta ya rasu shekaru ukun da suka shige, yana mai sheharu talatin da biyar a duniya. Ita kuwa Hajiya Umma Tukur Unguwar Sarki ta na da yara 7 wadanda dukkanin su ke fama da amosanin jini. Ta ce “kafin wata 9 suke nuna alamun ciwon, kuma su na bukatar abincin mai kyau, a kullum su na cikin rigar sanyi saboda ba sa san sanyi, ba sa san wahala”. Wannan uwa ita ce ke kici-kici domin tabbatar da yaran ta suna cikin yanayin da zai hana ciwon ya tashi, abunda ake kira da turanci "crisis” kamar yadda ta shaida.

Watanni biyu da suka shige ni ma wata aminiya ta a Kano ta hadu da rashi sakamakon wannan cuta. Mahmud Kyauta dan aminiyar ta wa ya rasu yana mai shekaru 19 a duniya. Zai shiga jami’a a bana amma sai ciwo ya tashi, aka kai shi asibiti a Kano, cikin ‘yan sa’o’i kadan Allah yayi masa cikawa.

A matsayi na na uwa, na ji wa aminiyar tawa. Domin rashin da mai shekaru 19 a duniya ba karamin abu bane. Na yi ta kokarin ba ta magana da nufin kwantar mata da hankali...dadin abun, a gida, arewacin Nigeria, dangi da makobta kan taimaka a irin wannan lokaci mai wahala. Kodayake dai imani da Allah shine ma babban kushin dake tausasa zuciya.

Sai dai abunda na fahimta shine duk da hanyoyin samar da bayanai na zamani, ga kuma uwa-uba radiyo, har yanzu jama’a a yankin arewacin Nigeria suna da karancin sani ko ilimi kan wannan cuta, wadda ko shakka babu ke ragargazar iyaye da yara.

Amosanin jini in ji masana, cuta ce da ake gada daga iyaye. A takaice matsale ce dake hana zagayawar iska Oxygen a jinin dan Adam. Wannan rashin zagaye na Oxygen a jini kan haifar da ciwo mai tsanani ga mai cuta. Ciwon kan tashi ne musamman idan mutum ya na fama da mura, ko wata ‘yar larurar ko kuma idan ma yayi wani aiki da ya jigata shi.

Masana suna cewa amosanin jini kan kawo lalacewar wasu mahimman injinan dake motsa jikin bil Adama kamar hanta, koda, huhu, zuciya da fatsarmama – abunda kuma suke janyo matsanancin ciwo a kasusuwa jiki. Masu amosanin jini kan yi saurin kamuwa da wasu cututtukan na daban saboda gaukuwar jikin su ba ta da karfi – ma’ana suna da saurin laulayi.

Daga jerin wadannan matsaloli zaka fahimci cewa duk iyayen da Allah ya baiwa yaro ko yara masu fama da amosanin jini, to lallai jidali ya same su.

Anan Birtania akwai babbar kungiya ta masu fama da kuma kula da cutar amosanin jini. Bayanai daga shafin su na intanet ya nuna ba sa kasa a gwiwa wajen gudanar da ayyukan da suka hada da ilmantarwa, wayar da kai, tarukan karawa juna sani, kafa gidauniya dan gudanar da ayyukan bincike kan cutar da dai sauransu. Bayanan kungiyar suka kuma ce babban abunda suka yi imani da shi shine, duk masu cutar amosanin jini na da ‘yancin a basu kulawar da ta kamace su. Suka kuma ce ba sa nuna kyama ko banbanci dan kai “dan kasa ne” ko a’a; ko kuma dan jinsin ka daban da na turawa.

Wannan abun sha’awa ne kwarai, kuma ya sa ni na yi tunani a game da labarin da BBC Hausa suka bayar na kokarin da kungiyoyi irin wadanda aka yi rahoto akan su a yau suke yi a Arewa, wajen samar da yanayi kwatankwacin abunda na karanta a shafin intanet din kungiyar amosanin jinin Birtania.

Amma babban abunda ya sanyaya mun jiki shine sanin cewa harkar kiwon lafiya a Nigeria musammman ma a Arewa din ta na cikin halin da bai dace ba. Muna fama da karancin likitoci, kayayyakin aiki, magunguna da ma dakunan shan magani a yankunan karkara. Haka kuma saboda taluci ya yiwa jama’a katutu, so tari ma iyaye hakura suke yi da kai yara asibiti. Abunda ya ta’azzarar lamarin shine masu fama da cutar amosanin jini na bukatar abinci mai gina jiki saboda kara masu kuzari da rage masu yiwuwar kamuwa da cuttuka. A zahiri dai jama’a na fama da abunda zasu ci sau daya ma a rana. Kididdigar Majalisar Dinkin Duniya ta shekarar 2007 na cewa kashi 70 cikin 100 na ‘yan Nigeria na rayuwa a kasa da dalar Amruka guda a rana wato Naira 140.

Tambayoyi anan sune: yaya jama’ar yankin arewacin Nigeria zasu tunkari matsalar cututtuka ba wai kawai amosanin jini ba, a’a har ma da sauran cuttuka barkatai da jama’a – yara da manya – ke fama da su? Yaya mahukunta zasu samar da ‘yancin jama’ar su na ba su kiwon lafiyar da ya kamace su a matsayin su na ‘yan Adam da kuma ‘yan kasa? Hakkin wanene ya tabbatar da cewa hukumomi sun cika aikin su na kare hakkin jama’a, tare da sauke nauyin dake kansu? Su kuma al’ummar mu wace rawa zasu iya takawa? Ta yaya zasu taimakawa kansu wajen samun hakkin su na ingantaccen kiwon lafiya? Shin mazaje na bayar da tallafi ga matan su, ko kuwa suna sakarwa matan duk nauyi da wahalhalu ta yadda a wasu lokuta matan ke rasa inda zasu saka kan su? A game da cuta amosanin jini, suna sane da cewa idan suka yi gwajin jini kafin su yi aure zasu iya kaucewa samun yaran da zasu kasance masu fama da cutar?

A tunani na wadannan kadan ne daga cikin dinbim tambayoyin da ya kamata mu yi kokarin amsawa wajen tunkarar cutar amosanin jini da sauran cututtuka a Arewacin Nigeria.

Saturday 27 February 2010

Zamani Riga



Allah dai shi yake kawo zamani. Kuma lallai tun da ya ba mu kwakwalwar yin tunani wajibi ne mu yi amfani da ita domin mu ga yadda zamu iya cin gajiyar abubuwan zamani domin samun ci gaba. Idan an ce ci gaba ba wai kawai samun alheri na duniya ba. A’a harma na lahira.

Lallai ci gaba ta fannin fusaha ya kawo abubuwa da yawa. Ya kawo gagaruman ci gaba ga rayuwar dan Adam. Babbar abar da kowa ke magana akan ta a wannan zamani da muke ciki ko kuma karni na ashirin da daya (21st Century) itace duniyar Gizo ko kuma Intanet. Bincike kala-kala ne suka kai ga samun intanet a duniya. Wadanda suka fi yin fice su ne wadanda Donald Davies da Paul Baran da Leonard Kleinrock suka yi. A 1982 ne aka fara jin kanshin abunda ake kira yanar Gizo a kasuwa. Amma sai a shekarun 1990 ne yanar Gizo ta bunkasa. A yau wasu na kiran wannan gagarabadan ci gaba da sunan “juyin-juya-hali”. Ina mai yadda da wannan ikirari domin kuwa a yau kusan babu bayanin da dan Adam zai nema ya rasa a intanet.

Duk da samun nasara a shekarun da yanar Gizon ta kunno kai, masu bincike a kasashen da suka ci gaba ta fannin fusaha sun ki komawa waje guda suce “ai mun ci galaba, bari mu tsaya anan”. A’a sai suka ce bari kuma mu duba yadda wata fusahar zata iya hawa kan wannan nasara da muka samu domin muga kuma inda sabon gwajin zai kaimu”. A sabili da haka ne masu bincike a dakunan bincike na jami’o’i da kamfanoni a kasashe kamar su Amurka, Japan, Sweden, Birtania, Faransa, Germus da sai sauransu, suka shiga gasa da juna wajen kera wayoyin hannun (salula) da zasu iya daukar fusahar intanet. Dama dai tuni irin wadannan wayoyi sun fara siddabaru kamar aikewa da sakonnin tes (text ko sms) da kuma daukar hoto.

A yau wayoyin zamani na aikewa da sakonnin murya da tes, kana suna nadar magana, daukar hotuna da bidiyo. Har wa yau suna da dakunan ajiye bayanan da suka hada da dubban lambobin wayoyin jama’a da sauti. Alal misali zaka iya adana gabadayan Al-Kur’ani mai tsarki akan wayar salula.

Riba ga al’umma ta dangane da wannan ci gaba ba kadan ba ce. Ka iya samun bayanai iri-iri ciki harda kayan koli ko masarufi, firashin kayayyaki, kasuwanni, asibitoci, makarantu da sauransu. Yanzu kuma kafafen yada labarai kamar su BBC, CNN, Al-Jazeera da sauran su, suna kutsawa inda suke neman tabbatar da samar da rahotanni ta hanyoyi daban-daban (wato sauti, tes, hoto da bidiyo).

Dama dai Hausawa mutane ne masu neman ilimi da san sanin abunda duniya ke ciki. Wannan ne ma ya sa suke ma’abuta sauraron radiyo. Abun sha’awa shine sun karbi sabuwar fusahar intanet da wayar salula da hannu bi-biyu, inda suke samun labarai, rahotanni tare da yin musayar ra’ayi da jama’a ba wai kawai a kauyukan su, ko garuruwan su ko kasashen su ba. A’a har ma a duk fadin duniya.

Ni ina ganin idan muka tsaya muka dage wajen amfani da fusahar zamani ta hanyoyi masu kyau, to kuwa babu shakka damu zamu samu gagarumin ci gaba a rayuwar mu kuma mu yi gasa da kowacce al’umma a duniya.

Kada na manta: BBC za ta gabatar da wasu jerin rahotanni na musamman na tsahon makonni biyu kan yadda intanet ta zama gababadau a wannan zamani na mu. Dan samun karin bayani sai kuje wannan shafin: http://bbcsuperpower.com/

Banbancin Mutum da Dabba


Da sunan Allah mai Rahama da Jin Kai. Na fara wannan kundi ne da nufin bayyana tunani na, da fahimta ta a game da abubuwan da na ci karo da su a rayuwa.

Shi dai Mahaliccin mu ya bamu kwakwalwa domin yin tunani kuma so tari ina jin ana fada tun ina karama cewa banbancin mutum da dabba shine tunani. A lokacin da nake girma sai nake nazari akan wannan furuci: "banbancin mutum da dabba shine tunani". Hakika haka maganar take.

Sai dai kuma da girma ya zo mani musamman bayan da na fara rayuwa a kasar yammacin duniya inda dabba take da hakki kusan daidai da na bil Adama, sai na fara kallon dabba daga wani bangare. Tun sannan na gano cewa ashe itama dabba tana da tunani kamar mutum. Alal misali ta san mai ba ta abinci, ta san mai korar ta. A sannan ne kuma na fara tunanin cewa mai yiwuwa banbancin mutum da dabba shine: mutum yana iya wasu abubuwa wadanda dabbobi basa yi kamar ikon magana da rubutu da karatu.

Wannan shine arzikin da dan Adam yake da shi: ikon tunani, mu'amala da sauran jama'a, karatu da rubutu, sannan ya hada wadannan hikimomi domin ciyar da rayuwar sa gaba.

Ci gaba shine ginshikin rayuwar mutum. Babu wanda yake san halin "jiya-i-yau". Ko rashin lafiya mutum ke fama da shi yana neman samun sauki, idan Taro kake da shi kana neman ya zama Sisi, idan tumakin ka biyu kana so su zama shidda, idan makota kake shiga debo ruwa to kana san Allah ya hore maka ta yadda zaka haka taka rijiyar a cikin gidan ka, idan a unguwar ku tsibirin shara ya dame ku kana so hukuma ta kirkiro da wani shiri da zai tabbatar da tsaftace muhallin ku...Tambayar anan itace shin kai da ni da kowa na amfani da irin hikimomin da Allah ya hore mana a matsayin mu na bil Adama wajen kawo ci gaba, ba ga rayuwar mu kawai ba, a'a, har ma ta al'ummar mu gabakidaya? A zahiri akwai ayar tambaya.

Mai yiwuwa tunanin ku ya banbanta da nawa...amma ni a ta wa 'yar fahimtar wannan shine tunani dan kalilan na Almajira.

Almajira


Wannan kundi zai dora duk wani abu da ya shafi ci gaban dan Adam daga fahimtar Almajira daga yankin Arewacin Nigeria.