Friday 11 February 2011

Juyin-Juya Hali a Masar: Talakawa Sun Yi Nasara


Shi kenan ta faru ta kare. An kafa tarihi a Masar. Jama’ar kasar ta Masar sun yi nasarar kifar da gwamnatin shugaba Hosni Mubarak, mutumin da ya shafe shekaru 30 ynla wadaka da kasar Masar din.

Tsagwaron juriya da dagewa da tirjewa da kuma tsabagen hadin-kai sun tattara miliyoyin jama’a a sassan kasar daban-daban dan nuna cewa sun kai karshen lamba, dangane da lamuntar kama-karyar da shugaba Mubarak yake yi masu. ‘Yan Masar sun shafe kwanaki gome takwas suna kwana bisa titi, suna cewa lokacin Mubarak ya kare…Allah raka taki gona!

Abubuwa da yawa sun taimaka wajen cimma wannan buri na Misirawa. Baya ga dagewar jama’ar, da akwai juriya da hakuri da shan wahala… amma uwa-uba shine sadaukar da kai. Da yawa daga cikin jama’ar Masar din sun san cewa mai yiwuwa rikicin ya ritsa da su – ma’ana, mai yiwuwa su rasa rayukansa. Wannan, bai hana su tsaya kan bakan su ba. Kuma a zahiri daruruwan sun hallaka din.

Wani abu kuma da ya fito fili shine fusahar zamani ta taimaka wajen tattaro masu irin wannan buri. Miliyoyin jama’a sun ta amfani da na’urar internet da wayoyin salula wajen yada manufofinsu, kana suka yi ta amfani da dandalin muhawara da musanyar bayanai na facebook da twitter da sauransu, wajen fadada kamfe din su.

A karshe dai kamfe din nasu ya mamaye kusan manyan biranen kasar, inda a kwanakin baya-bayan nan kungiyoyin ma’aikata su ma, suka shiga yajin aiki na sai-illa-masha-Allahu. Hakan ya karawa masu zanga-zangar kaimi, inda suka gano cewa, suna kara samun goyon baya daga jama’ar Masar din.

A karshe dai abunda ya faru a Masar juyin-juya hali ne mai matsanancin tarihi; wanda kuma zai yi tasiri a duk fadin duniya.

Babban sakon juyin juya halin Masar shine: KAN MAGE YA WAYE!

Mulki a hannun jama’a yake, ba’a hannun shugababanni ba. Ko shakka babu, wasu shugabannin da suka maida mulki tamkar kayan gado, zasu fuskanci makoma irin ta Hosni Mubarak.

Bari mu zura idanu mu ga wacce kasa ce zata biyo bayan Masar dangane da sabuwar iskar juyin juya halin da yanzu haka take kadawa a duniya!

Allah ya baiwa talakawa sa’a amin!

Friday 4 February 2011

Zanga-Zangar Masar: Ashe Mulki a Hannun Talakawa Ya Ke?


Yau a shirin BBC Hausa na Safe Nafisa Ahmed tayi wani rahoto wanda a cikinsa take tsokaci kan yadda karfin hadin kai tsakanin al'umma ke taka mahimmiyar rawa wajen juya akalar al’amuran siyasa a kasa. Nafisa tana bayani ne kan abubuwan da ke faruwa a wasu kasashen gabas ta tsakiya, amma musamman a Masar.

Jama’ar Masar sun yankewa kansu shawarar fitowa kan titinan babban birnin Alkahira da ma wasu biranen kasar, domin nuna kosawarsu da mulkin shugaba Hosni Mubarak, wanda ya shafe kusan shekaru 30 akan karagar mulki.

Jama’ar Masar sun jurewa mulkin Hosni Mubarak na tsahon wannan lokaci. Duk da haka kada a manta da rawar da tsohon sojen ya taka a harkokin mulki da tsaron kasar shekara da shekaru. Sai dai kuma a shekarun baya-bayan nan jama’a sun fara kaiwa magaryar tikewa da shugaba Mubarak.

Wannan kuwa na da nasaba da halin yanayin rayuwa a kasar ta Masar. Akwai matsaloli kamar talauci da rashin aikin yi musamman ma a tsakanin miliyoyin matasan kasar da kuma taka hakkin bil adama. Ga shi kuma uwa-uba ana zargin Mubarak yana shirin maida mulkin kasar na gado – wato ya nada dansa Gamal Mubarak a matsayin wanda zai gaje shi.

A takaice dai jama’ar Masar sun tsaya tsayin-daka ne, suna masu jajircewa mulkin danniya, zalunci da kuma yiwa tsarin democradiyya karen tsaye.

A karshe dai abunda ake hasashe zai faru a Masar din shine ra’ayin jama’a zai yi nasara akan ra’ayin mutum guda.

Yanzu haka saura kiris Hosni Mubarak ya zama tarihi a siyasar Masar. Sai dai abun takaici shine yadda bai yi hakan ba cikin daraja da mutunci; a’a sai da jama’ar kasar suka yi masa korar kare.

Wannan ba karamin darasi ne ba ga shugabannin kasashe, musammanma a kasashenmu, inda shugabani kan maida mulki tamkar kayan gado.

Abubuwan da suka faru a Masar da Tunisia da sauran kasashen Larabawa a ‘yan makonnin nan, sun nuna cewa ko shakka babu, iko ba a hannun shugabanni yake ba, a’a a hannun talakawan kasa yake.

Abunda ya kamata talakawan su yi kawai shine jajircewa, da rashin nuna gajiyawa, nuna rashin tsoro, kana da gujewa tashin hankali a yunkurinsu na kawo sauyi a kasarsu, domin kwatar ‘yancinsu da tabbatar da mulki na gari.

Hausuwa dai sun ce “gani ga wane, ya ishi wane tsoron Allah”. Allah ya tabbatar mana da mulki na adalci da rashin cin zali a kasashen mu, amin.