Friday 11 February 2011

Juyin-Juya Hali a Masar: Talakawa Sun Yi Nasara


Shi kenan ta faru ta kare. An kafa tarihi a Masar. Jama’ar kasar ta Masar sun yi nasarar kifar da gwamnatin shugaba Hosni Mubarak, mutumin da ya shafe shekaru 30 ynla wadaka da kasar Masar din.

Tsagwaron juriya da dagewa da tirjewa da kuma tsabagen hadin-kai sun tattara miliyoyin jama’a a sassan kasar daban-daban dan nuna cewa sun kai karshen lamba, dangane da lamuntar kama-karyar da shugaba Mubarak yake yi masu. ‘Yan Masar sun shafe kwanaki gome takwas suna kwana bisa titi, suna cewa lokacin Mubarak ya kare…Allah raka taki gona!

Abubuwa da yawa sun taimaka wajen cimma wannan buri na Misirawa. Baya ga dagewar jama’ar, da akwai juriya da hakuri da shan wahala… amma uwa-uba shine sadaukar da kai. Da yawa daga cikin jama’ar Masar din sun san cewa mai yiwuwa rikicin ya ritsa da su – ma’ana, mai yiwuwa su rasa rayukansa. Wannan, bai hana su tsaya kan bakan su ba. Kuma a zahiri daruruwan sun hallaka din.

Wani abu kuma da ya fito fili shine fusahar zamani ta taimaka wajen tattaro masu irin wannan buri. Miliyoyin jama’a sun ta amfani da na’urar internet da wayoyin salula wajen yada manufofinsu, kana suka yi ta amfani da dandalin muhawara da musanyar bayanai na facebook da twitter da sauransu, wajen fadada kamfe din su.

A karshe dai kamfe din nasu ya mamaye kusan manyan biranen kasar, inda a kwanakin baya-bayan nan kungiyoyin ma’aikata su ma, suka shiga yajin aiki na sai-illa-masha-Allahu. Hakan ya karawa masu zanga-zangar kaimi, inda suka gano cewa, suna kara samun goyon baya daga jama’ar Masar din.

A karshe dai abunda ya faru a Masar juyin-juya hali ne mai matsanancin tarihi; wanda kuma zai yi tasiri a duk fadin duniya.

Babban sakon juyin juya halin Masar shine: KAN MAGE YA WAYE!

Mulki a hannun jama’a yake, ba’a hannun shugababanni ba. Ko shakka babu, wasu shugabannin da suka maida mulki tamkar kayan gado, zasu fuskanci makoma irin ta Hosni Mubarak.

Bari mu zura idanu mu ga wacce kasa ce zata biyo bayan Masar dangane da sabuwar iskar juyin juya halin da yanzu haka take kadawa a duniya!

Allah ya baiwa talakawa sa’a amin!

2 comments:

  1. Allah sarki hajiya jamila, ai hausawa sunce mai laya kiyayi mai zamani. dama Allah yayi alkawarin ruguza milkin kamaa karya in har mutane sun so, toko Allah yace zai taimakesu. idan ko sukla kwanta to Allah bazai canza musuba har sai sun canza da kansu!!!!. yanzu ya ragewa sauran kasashen Afirka. mun gode da wannan babbar gudun mawa. ki huta lafiya.

    ReplyDelete