Tuesday 5 April 2011

Kancal A Shirin Zaben Nigeria


Zaben Nigeria na ci gaba da jan hankali a ciki da wajen kasar saboda dalilai da yawa. Kuma yanzu, fiye da kowanne lokaci, na yi imanin cewa duk kokarin mutum na kawo gyara a kasarmu, sai wasu sun yi kokarin kawo cikas, ko yin kancal!

Kowa dai ya san Profesa Attahiru Jega shugaban hukumar zaben Nigeria wato INEC, mutum ne mai akida. Kuma idan ya dage kan abu, ba’a iya tankwara shi.

Allah dai ya kai shi INEC, kuma tun sannan wasu suke cewa mai yiwuwa saboda akidarsa a samu ingantattun zabuka a Nigeria. Sai dai kuma wasu na cewa shi kadai ba zai iya kawo gyara ba. Inda masu musun farko ke cewa ai shugabanci na iya sauya na kasa. Ni ma ina daga cikin wadanda suka yi wannan fata.

Sai dai yayinda ni da sauran abokan aikina a BBC muka shirya kawowa ‘yan Nigeria rahotannin zaben da aka shirya yi a 2 ga watan Afrilu, sai kwatsam rahotannin matsaloli. A karshe dai an dage zabukan.

Dage zabukan sakamakon cikas din da aka samu abu ne da ya girgiza mutane da yawa. Sai dai mafi yawan ‘yan Nigeria na ci gaba da baiwa Jega goyon baya, suna masu cewa muddin dai zabukan zasu kasance na fisabilillahi, to ai dage su ba wani ba ne.

Ana dai ta hasashe da zarge-zarge cewa akwai wasu da suka hadiyi layer cewa zabukan nan ba zasu yi nasara ba ko ta halin hakaka saboda dalilan san-kai ba na san kasa ba. Idan haka ne Allah ya yi maganinsu domin bayin Allah.

A karshe ya zaman wajibi jam’ar Nigeria su jajirce wajen tabbatar adalci da samun shugabanni na gari.

3 comments:

  1. Karshen jajircewa shine yadda yan kasa suke fitar dango wajen zabe. Abin tsoron shine yadda ake amfani da jamian tsaro wajen musgunawa yan adawa.Bayan haka ana amfani da kudi a wajen da N50 kacal, ka iya tasiri domin talauci yayiwa mutane katutu.

    ReplyDelete
  2. HAJIYAR TALAKAWAN NIGERIA ALLAH SHIKAREKI

    ReplyDelete
  3. Abdulkadir Sani Haka yake haj Jamila,domin duk kokarin da Jega keyi nakawo gyara a zaben Nigeria wasu bara gurbi nanan suna yimai zagon kasa domin an kama mutane da yawa da takardun zabe na bugi.Sabo da wannan na ke kira da talakkawa yan Nigeria da su sa ido sosai akan wannan zaben basani basabo.
    Tuesday at 16:05 · LikeUnlike · 1 person

    Garba Ayuba likes this.Muntari Abubakar Haka yake Hajiya. To amma fa talakawan Nigeria dolene mutashi tsaye mu dage da addu'o'i na musamman, domin dukkannin mai bin kafafen yada labarai na gida da wajen Nigeria ya kwana da sanin cewa da akwai matsaloli masu yawa dangane da zabe a... kasarnan. Don haka sai mu dage sosai wajen sake fitowa a sabin lokutan da aka fitar na zabe domin mu zabi shugabanni na gari da kuma stare kuru'ummu, kuma muci gaba da addu'ar Allah ya taimakama hukumar zabe wajen ganin ta kammala dukkannin shirye-shiryen da kamata kafin zuwan lokutan data fitar. ALLAH YA TAIMAKEMU GABA DAYA. AMEEN!!!

    Tuesday at 16:28 · LikeUnlikeGarba Ayuba jamila maganarki gaskiyane.aman dai ki sani akwai masu aniyar cewa inbasu ba a fasa kowa ya rasa.Allah dai shiyi maganin wadanda basason cigaban kasarmu nigeria.

    Tuesday at 16:38 · Buba Maigoro Gashua Jamila sai muce miki ameeeeeen,amma Nigeria sai Buhari insha Allahu.
    Tuesday at 17:36 ·

    Loading...Nafiu Usman Haj. Allah ya fisu @ Buba, 20011 sai Buhari and Bakari
    Tuesday at 17:59 · LikeUnlikeNafiu Usman Insha Allah
    Tuesday at 17:59 ·

    Muhammad Yabo haj, kinga dadin a shaidi mutum da halin kirki, jega yasamu saidar kwarai, hasalima har goyon bayansa kake jin tallakawa nayi. mu muka san haka mudake zaune cilin mutanen karkara. Allah gyara mana kasarmu najeriya.
    Tuesday at 19:46 ·

    Auwal Hassan Makarfi A gaskiya Hajiya Muna Bukatar Mukara jajircewa da Addua.Allah Ubangiji Yataimakemu Amin.
    Wednesday at 11:17 ·

    ReplyDelete