Tuesday 29 June 2010

Talauci na Janyo Mutuwar Mata Wajen Haihuwa


Da alama matsalar mutuwar mata sanadiyyar haihuwa, na ci gaba da ci wa al'ummar yankin arewacin Nigeria tuwo a kwarya. Kodayake dai wannan ba matsala ce da ta addabi kasar Nigeria kawai ba, a'a sauran kasashe masu tasowa musamman ma a nahiyar Africa su ma suna dimbin hasarar rayukan mata da jira-jirai. Alkaluman hukumar UNICEF na nuna mace daya daga cikin goma sha-uku na mata masu juna biyu kan rasa rayukan su a lokacin haihuwa a nahiyar Afrika.

A wani rahoton BBC, wakilin jihar Jigawa, Muhammad Annur Muhammad, ya bayyana cewa a shekaru ukun da suka shige, alkaluma sun nuna cewa jihar Jigawan ce kan gaba a Nigeria a wannan matsala.

A jihar Borno ma, mata na rasa rayukan su a kullum idan suka zo haihuwa. Duk da bayanan da suke nuna cewa an soma samun nasarar rage matsalar a wasu kasashen tun bayan rattaba hannun kan kudurorin Muradan Majalisar Dinkin Duniya na shekara ta 2015 da shuwagabannin kasashe 147 suka yi, har yanzu akwai jan aiki a gaban Bornon. Lamarin haka yake ma a sauran jihohin arewacin Nigeria. Kodayake dai an tabbatar da cewa shiyyar arewa maso gabashin Najeriyar ce da har yanzu alkaluma ke nuna matsalar tafi ta'azzara.

Amma kuma wasu jihohin arewacin Nigeriar na dan tabusawa. A jihar Jigawa, Mohammed Annur Mohammed na BBC Hausa, ya ce gwamnatin jihar ta shigo da wani shiri wanda ya kunshi horar da al'ummomi musamman na yankunan karkara su kafa wata kungiya da hukumomin ke ilmantar da su bisa hanyoyin kula da mata masu juna biyu, tare da ba su motoci don hanzarta kai matan asibiti.

Akwai matsaloli daban-daban dake janyo mutuwar mata masu juna biyu idan suka zo haihuwa. Babbar matsala dai ita ce talauci. Matan talakawa masu juna biyu sun fi yiwuwar mutuwa idan aka kwatanta da matan mazaje masu hannu da shuni. Saboda rashi, matan talakawa ba sa samun abinci mai gina jiki.

Baya ga wannan, sukan yi ayyuka na karfi, da wahala kamar su noma da surfe da sussuka, har zuwa lokacin da suke gab da zuwa kan-gwiwa. Karfin su kan kare a lokacin da haihuwar ta zo, wanda kuma a lokacin ne suka fi bukatar karfin.

Haka kuma mata marasa ilimi sun fi yiwuwar rasuwa wajen haihuwa fiye da mata masu ilimi saboda sun fi su sanin hanyoyin kaucewa daga wasu haddura; kana sun fi su sanin mahimmancin zuwa asibiti - tun daga lokacin awan ciki har ya zuwa lokacin haihuwa. Alal misali kididdiga ta nuna mata masu ciki biyu cikin goma ne kawai ke zuwa asibiti a jihar Jigawa a yayin da suke da juna biyu.

Matan dake zaune a kauyuka sun fi yiwuwar rasuwa a wajen haihuwa fiye da matan dake zaune a birane. Rashin asibitoci a kauyuka ko kuma nisan da suka yi daga birane na nufin mata masu juna biyu basu cika samun kulawa cikin hanzari a lokacin da suke nakuda ba. So tari kan a je asibiti, sai ka ga rai yayi halin sa. So tari ma har da na jaririn.

Muddin dai yankin Arewacin Nigeria na san cimma manufofin raya kasa, bunkasa da tattalin al'ummar su, ya zama wajibi su tashi haikan wajen tabbatar da daukar matakan da zasu magance wannan matsalar dake janyo hasara mai dimbin yawa ga yankin. Saka idanu wajen kula da jama'a, musamman talakawa babban hakki ne da ya kamata su sauke.

No comments:

Post a Comment