
Yanzu haka an fara shiga yanayin siyasa a Nigeria wato yayinda ake shirin gudanar da zabukan shekara mai zuwa.
Siyasa na da mahimmanci a kowacce kasa ta duniya dake bin tarafkin democradiyya. Dalili kuwa shine siyasar tsarin democradiyya na baiwa jama’a damar zabar wanda suke ganin ya dace da su, kuma wanda zai biya masu bukatun su da kuma share masu hawaye.
Jama’a kan ba da goyon baya ga wanda suka yi imanin zai wakilce su – kuma wakilci na gari – ba wanda zai je dan wakiltar kan sa ba. Ta yaya jama’a ya kamata su tabbatar da cewa sun zabi na gari ba zaben tumun dare ba?
Mai yiwuwa sai nan gaba zamu tattauna wannan batu. Amma ina so na yi a wannan sharhi ne akan siyasar banga.
Tun bayan da Nigeria ta koma tsarin democradiyya yau shekaru sama da goma ‘yan siyasar kasar ke amfani da matasa domin cimma manufofin su na siyasa. Ba laifi ba ne ‘yan siyasa su nemi goyon bayan matasa. Misali a baya-bayan nan, kuri’a da goyon bayan matasan Amruka ta taimaka gaya wajen nasarar shugaba Barack Obama a 2008.
Abunda yake laifi shine amfani da matasa a matsayin ‘yan bangar siyasa domin samun nasara a zabe. A zabukan da suka wakana a baya ‘yan siyasa a Nigeria na baiwa matasa kudi, inda su kuma sukan sayi kwaya da sauran ababen sa maye da makamai, suna bi suna razana abokan hamayya da sauran jama’a.
Kamar yadda na gani a wannan hoto dake kan wannan shafi (wanda na dauka sa’ilin da na kai ziyara Bauci a watan jiya), rikici kan rincabe tsakanin ‘yan bangar siyasa. Akan yi fito-na-fito tsakanin ‘yan bangar ‘yan siyasar. Wani lokaci a ji munanan raunuka, a wasu lokuta a rasa rayuka. Wannan abun takaici ne.
Shin matasan nan da suke bari ana amfani da su dan cimma manufar zabe, duk da cewa sun san ‘yan siyasa zasu yi watsi da su, da zarar sun yi nasara, sun san ciwon kan su kuwa? Suna da masaniya kan cewa ‘yan siyasa basu damu da su ba illa kawai sun mai da su tamkar matattakala ce da suke takawa domin “cin zabe” ko ta halin kaka?
Amsar da nake san sani itace: ta yaya ne matasa zasu jajirce su ki yarda ana amfani da su a matsayin ‘yan bangar siyasa a bisa kudi kalilan – wadanda akewa kallon marasa mutunci a Nigeria - lamarin da ka iya sanadiyyar hasarar rayukan su da ci bayan kasar su?