Sunday 4 April 2010

Jiki Magayi - Talaka na Mutuwa a Rikice-Rikice


Rikicin addini da na siyasa sune manyan labarun dake janyo fargaba ga Edita ko shugaban kafar yada labarai. Alal misali wajibi ne na tabbatar da cewa mun bada labarin rikice-rikicen addini da kabilancin ba tare da nuna san zuciya ga kowanne bangare ba. Haka ma rikicin siyasa.

Babban abunda na lura da shi a aikina shine a Nigeria kusan kashi casa’in cikin dari na rikice-rikicen da ake yi, manya ne suke ta da su. Manya sun hada da wasu masu kudi, da wasu malaman addini na Musulunci ko Kirista, da wasu ‘yan siyasa.

Tun lokacin da Nigeria ta kama bin hanyar democradiyya a 1999, kasar ta yi fama da rikice-rikicen addini da kabilanci daban daban. Tun daga rikicin OPC Shagamu, Kano, Zangon Kataf, Tibi, Yalwan Shandam har zuwa na baya-bayan nan, wato su Boko Haram, Kala Kato da kuma rikice-rikicen Jos.

Masu bincike sun yi ittifakin cewa manya na da hannu a wadannan rikice-rikice. Suka ce wannan ne ma ya sa aka ki hukunta kowa.

A hirar da na yi da shi a BBC Hausa, tsohon sarkin Gwandu Alhaji Mustapha Jakolo ya yi tambaya mai mahimmanci. Ya ce “kin taba jin wani babban mutum, ko shugaban addini na Musulmi ko na Kirista da aka kashe, ko kuwa ‘ya’yan su? A kullum aka tashi masifa a Nigeria, hasara na tsayawa ne ga talakawan kasar.”

Wannan maganar haka take. Da na je Jos a kwanannan, ilahirin hasara – ta rai da dukiya – ta kare ne kan talaka. Wannan ne ma ya sa ni tambayar: me yasa talakawa ba zasu gano cewa wasu na amfani da su ba ne domin cimma wata manufa? Wani da wahala, wani da riba – shine abunda ke faruwa.

Abunda zan so in ji daga gareku shine: yaushe ne talakan Nigeria zai koyi darasi? Yaushe ne zai daina yarda wasu manya suna amfani da shi, kuma a karshe hasara rai ko ta dan abunda suka mallaka ta komo kansu? Yaushe zai ce, “idan kana so muyi kashe-kashe bamu ‘ya’yan ka mu je tare”?

Lokaci yayi da talaka zai jajirce ya ki karbar ‘yan tsirarun Nairori dan biyan bukatar wasu da a zahiri basu damu da su ba, domin iyalan su na turai su na karatu ko shakatawa da kudaden da ake zargin sun kwashe na su talakawan.

Hausawa dai suka ce jiki magayi.

4 comments:

  1. A gaskiya ne wannan Hajiya, Abin da kamar wuya gurguwa da auran nesa. Wayannan darusa bazasu karantuba har sai mun kawar da kwadayi da san abin hannun shuwaga banni da attajirai, mu tashi mu nemi sana'a domin yan zaman banza sune babbar silar hura wutar rikici don samin ganima, mu kaunaci junan mu mu cire kabilanci musamman agun sana'oin mu. Haka kuma sai mun kyamaci duk wani mai san jefamu hanyar halaka, dole ne sai mun yiwa kanmu fada akan shuwaga bannin da muke zaba don zabar shugaba na banza na samun al'umma gurbatacciya. Yan uwa'na kada mu manta kasa daya al'umma daya, muyiwa kanmu hisabi kafin a mana. Dafatan Allah ubangiji ya kawo kauna da zaman lafiya a kasarmu Najeriya. Aliyu M Umar Kwalli Kano

    ReplyDelete
  2. To talakawa lokaci dai sai kara motsowa yakeyi.ya kamata kan mage ya waye,mu daina kula da dan abinda mugayen shuwagabanni ke bayerwa mu dage damtse mu zabi shuwagabannin kirki domin ci gaban kasarmu nigeria.Allah yasa mudace ameen.

    ReplyDelete
  3. To abinda za muce Allah (S.W.A) ya kawo mana shugabannin da zasu so mu, suyi kishin mu kamar yadda zasu so kansu da 'yayansu.
    Kuma Allah ya sa jama'a su gane masu son su da kuma makiyan su.

    ReplyDelete
  4. To Hajia wannan haka ne, to ai wannan ni aganina duk rasin fahimta ne, saboda sai in mutum ya na da fahimta yake ganewa. Ai talauci ba hauka bane, amma rasin fahimta yafi hauka muni.
    Duk wanda yake da fahimta ba zai kashe dan uwansa ba ko ya
    bàta dukiyar wani. Ya kamata gwamnatoci Afrika susa masu fahimta su rika shiga lungu lungu,
    a fahimtar da mutane, su san ma'anan demokradiyya da cevilization. Sune ka so dan uwarka kuma kuyi aiki tare. wassalam Alhaji pastor daga Belgium

    ReplyDelete