Wednesday 15 June 2011

EFCC KO KYANWAR LAMI


Yau shugabar hukumar yaki da laifukan da suka danganci ta’annati da dukiyar jama’a a Nigeria wato EFCC ta yi bikin cika shekara 8 da kafuwa. Shugabar ta zayyana irin kokarin da hukumar ta su ta yi, wajen zakulo wadanda ta kira miyagun da suke wawaso da dukiyar jama’a.

Hukumar ta kara da lasafta sunayen manyan mutane, musamman ma tsoffin ministoci da gwamnoni da wasu ‘yan kasashen waje da suke da uwa a gindin murhu- wato manyan jami’an gwamnatin Nigeria - a matsayin shaidar kokarin da suke yi na sa kafar wando guda da duk wannda ya yiwa dukiyar Nigeria karan tsaye.

Lallai wannan ba karamin abu bane a kasar da cin hanci ya zame mata jini da tsoka. Ko a cikin ‘yan kwanakin nan sai da jami’an tsaro suka yi artabu da tsohon kakakin majalisar wakilan kasar Dimeji Bankole kafin su kama shi a makon jiya. Hukumar EFCC din na zargin Bankole da barnatar da kudin da suka haura Naira biliyan 40.

A gaskiya dai duk da kokarin da EFCC ta ce tana yi, jama’ar Nigeria na ci gaba da yi mata kallon wata wadda ke da manufa ta karkashin kasa. Allal misali a yanzu haka da akwai wadanda suke zargin cewa wai ana tuhumar Bankole ne saboda ya ja ragamar ‘yan majalisar da suka sauya dokar zaben kakakin majalisa. Shi kuma wannan sauyi da majalisar ta yi, shi ya kai ga wancakalar da shirin karbi-in-karba, lamarin da ya batawa jam'iyyar PDP rai.

To, ko ma dai wane kallo ake yiwa EFCC, mutane masu yawa na ganin, kamata yayi hukumar ta daina kwakwazo, ta kama mutum, kana sai a ji shiru. A madadin haka idan aka kama mutum, sai a kaishi kotu, a yanke masa hukunci, sannan a bayyanawa jama’a hukuncin da aka yanke masa, saboda ya zama darasi ga saura. Har yanzu kalilan ne a cikin manyan mutanen da EFCC ta bayyana sunayen su aka gurfanar da su gaban kuliya kana aka yanke musu hukunci. So tari maganar shiriricewa take yi kawai.

A karshe muddin dai EFCC na san ta yaki ta’annati da dukiyar jama’ar Nigeria, to wajibi ne ta tabbatar ta ga karshen zargin wawason da ake yiwa mutane, sannan ta bayyanawa duniya hukuncin daurin da aka yiwa mutum. Baya ga wannan sai kuma sauran hukumomi su buga sitamfi akan mutumin nan da aka yankewa hukuncin, da cewa: muddin aka kama ka da laifi, kana aka hukunta ka bisa laifin satar dukiyar bayin Allah, to kuwa kayi sallama da rike mukami a Nigeria, komai kankantarsa.

Muddin ba’a yi haka ba, kowa zai ci gaba da kwasar ganima saboda ya san cewa bayan an kamala hayaniya a kafofin yada labarai, zai kwana kalau. Watakila bayan ‘yan watanni ya tsaya takarar mukami, kuma a ganshi mirsisi wai yana rike da matsayin mai yin doka a kasa, ko ya zama shugaban al’ummar da ya taba cuta a matakin jiha ko kasa.

A yayinda ta cika shekara 8 da kafuwa, dole EFCC ta guji kasancewa Kyanwar Lami.

6 comments:

  1. This comment has been removed by the author.

    ReplyDelete
  2. lalle kam kyanwar lami: ita bata yakushi kuma ita bata cizo. ai Hajia a nawa ganin ma EFCC aikinta na banza ne a Najeriya, domin karnukan farauta ne da Gwamnati ke amfani da su a lokacin da bukatar hakan tazo. Abin da nake da tantama shine, dukiyar da take kwato wa a hannun wayanda take zargi da ta'annati ina take kaisu ne? a aljuhun gwamnati take zubawa ko kwa a aljuhunta take ajjewa? gaskiya EFCC ta wuce kyanwar lami a gani na. A M Umar Kwalli

    ReplyDelete
  3. wannan sharhi yayi matukar bugeni, Allah ya taimakeki yakuma baki karfin gwiwa don kicigaba da irin wannan rubutu mai amfani

    ReplyDelete
  4. Hakika EFCC ta yi kama da kyanwar Lami kuma kayar farautar 'yan adawar siyasa fakat. Daga ka ji an ce EFCC na tuhumar wani to ba a raba daya biyu ka tarar in ma dai abokin adawa ne ga mahukunta ko kuwa wanda ya ki bada hadin kai garesu don cimma wata manufa.
    Babban abin takaici shine, tun kafuwar EFCC ba wanda zai ce ga abinda akayi da kudaden da take cewa ta kwato. Haka kuma ba wanda aka hukunta a hakikar gaskiya. Saboda haka hukumar dai holoko ce.

    ReplyDelete
  5. Yanzu haka gashi takaddama ta barke a tsakanin tsaffin shugabanni hukumar ta EFCC, tare kuma da mutumin da aka kafa hukumar a lokacin mulkinsa wato Gen. Obasanjo.

    ReplyDelete
  6. Yanzu haka gashi takaddama ta barke a tsakanin tsaffin shugabanni hukumar ta EFCC, tare kuma da mutumin da aka kafa hukumar a lokacin mulkinsa wato Gen. Obasanjo.

    ReplyDelete