Friday 15 July 2011

Ga Tashin Bama-Bamai ga Watan Ramadan



Halin da ake ciki yanzu haka a wasu yankun nan Arewacin Nigeria musamman ma Maiduguri ya kai abunda zamu ce “Inna Lillahi wa inna ilaihir rajiun”. Tashe tashen hankula sakamakon tashin bama-bamai da kuma samamen da ake kaiwa kan wadanda ake zaton yan kungiyar Boko Haram ne sun sanya matsanancin tsoro da fargaba a zukatan jama’a.

Ana ta muhawara kan yaya aka yi har aka kai wannan mummunan hali da ake ciki. Ni a ganina wannan ihu ne bayan hari. A madadin tambayar yaya aka yi aka kai haka. Kamata yayi a maida hankali kan yadda za’a samo maslaha domin kawo karshen wannan hali da ake ciki.

Sai dai kuma ko wannan ma ba karamar tambaya ba ce. Shin yaya ake ganin za’a iya magance matsalar? Ta ina za’a faro? Shin tattaunawa ya kamata ayi? Idan tattaunawa ce tsakanin wa da wa za’a yi? Kuma idan za’a yi tattaunawar su wanene zasu wakilci gwamnati, su wanene zasu wakilci ‘yan kungiyar ta Boko Haram?

A jiya an rawaito kungiyar tuntubar juna ta Arewa wato Arewa Consultative Forum ta na cewa zata baiwa shugaban Nigeria Goodluck Jonathan shawara kan yadda ta ke ganin ya kamata a tunkari matsalar ta Boko Haram.

Sai dai a wani lamari tamkar arashi, a yau sai kungiyar matasan Arewa wato Arewa Youth Forum suka fitar da wata sanarwa suna masu kakkausar sukan dattawan na Arewa. Suka ce ai dattawan basu da hurumi, halarci ko iyawa a game da yadda za’a warware matsalolin Arewa. Kungiyar ta ce ai tun da farko su dattawan Arewan ne suka jefa yankin cikin mummunan halin fatara da jahilcin da ake ciki. Amma yanzu kiri da muzu, sun zo su na maganar magance matsalar.

To lallai dai masifar da ake ciki a yankin Arewa ta Nigeria ba jiya ko shekaranjiya ta samo asali ba. Matsala ce da ta jima tana ci, can daga karkashi. A shirin BBC Hausa a Karkara na Maris 2009, na jagorancin ‘yan jaridar BBC Hausa inda muka ganewa idanuwan abubuwan da suka saka mu hawaye. A shirin BBC Hausa a Karkara na karshe na bayyana cewa Arewacin Nigeria na zaune akan bam wanda a kowanne lokaci zai iya tashi.

A wanncen lokaci wasu sun ce muna yiwa kasa mugun alkaba’i. Abun takaicin shine, sun kawar da idanun su daga halin talauci, rashin aikin yi, shaye-shayen miyagun kwayoyi, da watangaririyar da ‘ya’yan bayin Allah ke yi a yankin. A karshe ga halin da muke ciki a yau.

To babban jawabi na a wannan sharhi, shine, kamar kowa, ina yin roko na cewa yayinda watan ibada mai tsarki na watan Ramadan yake karatowa, shugabanni da ‘yan kungiyar Boko Haram, su dubi girma Allah Subhanu wata’ala, su nemi hanyar kawo zaman lafiya, hanyar da za’a wanzar da adalci tsakanin al’umma. Wannan shine kadai zai kawo zaman lafiya mai dorewa.

1 comment:

  1. Hajiya sannu da kokari hakika dukkan bayanan da ki kayi suna kan layi. fatana Allah ya bamu zaman lafiya a kasarmu.

    Yasir Ramadan Gwale.

    ReplyDelete