Sunday 21 March 2010

Ana Ga Yaki Suna Ga Kura


Babu shakka kasashe masu tasowa na fama da dimbim matsaloli. Mafi yawan wadannan matsaloli kuma mutane ne ke janyo su – ba wai Allah ne ke doro su ba. Kodayake dai kusan a kowanne lokaci mu kan danganta abubuwan mu ga kaddara, amma kuma wajibi mu kasance masu taya Allah kiwo.

Ina Kano a ranar da gobarar ta tashi a kasuwar kantin Kwari. Na isa kantin Kwarin bayan da mai aikowa da BBC rahotanni daga Kano, Yusuf Ibrahim Yakasai ya bugo mani waya jim kadan bayan misalin shida da rabi na safiya.

Koda na isa kantin Kwari sai na iske dubban mutane sun yi cincirundo, ana ta firmitsi-mitsi. Na ga wadanda nake zaton ‘yan kasuwa ne suna kici-kicin kwashe kayan su daga shagunan dake kusa da wadanda ke cin wuta – musamman ma dai gidan Labaran wanda a wannan lokaci yake ta ci da wuta.

Baya ga masu kokarin kwashe kaya, sai kuma ga ‘yan kallo. Wadannan sune mutanen da suka ba ni mamaki. Su wadannan mutane samari da manya, sun je wajen gobarar ne wai dan kashe kwarkwatar idanu. Yawan ‘yan kallon ya sanya an samu cunkoso a bisa ‘yar siririyar hanyar da ita ce masu motar kashe gobara za su bi.

‘Yan kallon ba su yi tunanin cewa gobara ba abar kallo ba ce, da kuma cewa suna saka rayuwar su da lafiyar su a cikin hadari. A yadda na ga ginin ke ci da wuta, kiris yake jira ya ruguzo kasa. Ina cikin wannan tunani sai na ji ana “ku gafara, ku gafara, ginin zai fadi”.

Sai rududu...jama’a suka fara gudu. Allah dai ya kiyaye firmitsi-mitsin bai kai ga jikkata ko hallakar kowa ba.

Wani abu da na lura da shi a lamarin gobarar kantin Kwarin kuma shi ne aikin tsarin ceto idan wata masifa ta auku a Nigeria. Ni dai har na bar wajen, motar kashe gobara kwaya daya kacal na gani (kamar yadda wannan hoto ya nuna). Kuma ban ga ta na feshin ruwa a lokacin da naje ba. Da na yi tambaya sai aka ce wai babu ruwa amma ana jira za’a kawo.

Bayan wani lokaci na bar wajen. An dai ce ruwa ya samu isa, kuma an samu kashe gobarar da ta fara ci tun karfe daya na safe har zuwa misalin bayan azahar – wato wajen sa’o’i 12-14 kenan. Ganin tsukukun wajen, Allah ne kawai ya takaita ta’adi da hasara.

Idan akwai masu lissafin gobarar kantin Kwarin da ta faru a wannan watan, to wajibi ne su yi nazari kan batutuwa da dama da nufin daukar darussa domin kiyaye gaba. Kadan daga wadannan su ne:

Ya kamata kayayyakin ceto da agaji kamar na kashe gobara su kasance a kowacce kasuwa ta yadda ba sai gobara ta tashi ba za’a shiga nemo mota da ruwan kashe ta?

Shin ginin kasuwannin mu ne irin na zamani ne ta yadda zasu kasance an samu raguwar masifu kamar gobara da ambaliyar ruwa?

Akwai hanyoyi masu fadi da za’a iya kaiwa ga kantina ba tare da masu aikin agaji ko ceto sun samu matsala ba?

Ya kamata jami’an tsaro kamar su ‘yan sanda su shiga aikin killace wajen da matsalar ta afku saboda hana ‘yan kallo cushe wajen?

Shin akwai wata hanya da za’a ragewa wadanda irin wannan masifa ta afkawa radadi wato ta hanyar basu tallafi? Domin kuwa a ganina idan ba wani ikon Allah ba, gobarar nan ta kantin Kwari zata kasance karshen wasu kenan.

Mai yiwuwa idan muka tunkari wadannan batutuwa mu taya Allah kiwo.

Allah ya kiyaye.

7 comments:

  1. Allah ya kara kiyaye gaba. Wadanda sukayi hasara Allah ya mayar musu da alkhairi.

    ReplyDelete
  2. Hajjiya Jamila wadannan shawarwarin naki ababan lura ne. Da fatan hukumomi da mutanen da abun ya shafa zasu gyara. Wallahi mafi yawan matsalolin mu, mu muke jawo su da kammu kuma sannan mu ce kaddara ce ko kuma Allah ne ya kawo. Allah ya ganar damu gaskiya kuma ya bamu ikon binta.

    ReplyDelete
  3. This comment has been removed by the author.

    ReplyDelete
  4. Allah ya kiyaye Amin. Amma kam akwai kalu bale babba a gaban mu. Ni anawa tunanin, cunkoson `yan kallo yana nuna rashin aikin yi da yayi katutu acikin mutanen mu. Kuma ba karamin abin kunya bane ace gobara ta tashi irin wannan amma babu kayan aiki da za'a yi amfani da su a kashe wutar. wai shin mai nene tunanin shuwagabannin mu? shin wai su ko kunya basa ji bayan karairayin da suka shaf shafta wa mutane a karshen ace babu wani kyakkyawan tsari na kare mutane ballantana dukiyoyin su? kuma kasancewa ta Dan Kano, dan kasuwar kwari a wani lokaci na san yanayin rashin doka da ka'ida, da rashin tsari da ke cikin wannan kasuwar, ita kanta kasuwar ta cancanci ayi mata zazzaga kuma akawo karshen mugun nufi na wasu `yan kasuwan mu ta yanda zaka ga har kasan matakalar bene ma an yi mata kofa a matsayin kanti...Allah ya sauwake
    Abubakar Abubakar Usman
    Kuala Lumpur, Malaysia

    ReplyDelete