Saturday 27 March 2010

Tilin Shara a Biranen Mu


Ban sani ba ko wani zai gane wannan tilin sharar dake wannan hotan. To wannan dai wata unguwa ce a birnin da yafi kowanne girma a nahiyar Afrika. Wato birnin da na fito, birnin da aka haife, Kano.

Kusan ta kowanne bangare Kano shine birnin da ya fi kowanne birni a Nigeria. Wannan ma shi ya sa ake masa kirari da: Kano, ko da mai ka zo an fika. Sai dai kuma tsakani da Allah, ba komai ne ya kamata a ce birni na, yafi saura akai ba.

Ba alfahari ba ne a ce birni na shi ya fi kowanne kazanta ko tarin shara a Nigeria ko Afrika. Idan na zo da baki ina yawo da su a garin nakan ji matukar kunya. A gaskiya ma, akwai unguwannin da bana bi da su.

Na yadda kan cewa yawan jama’a na taimakawa wajen taruwar shara a kankanin lokaci. To amma musun da nake san yi anan shine, ai idan aka samar da wata hanya kyak-kyawa, mai tsari, ta kwasar shara akan kari, ba tare da bata lokaci ba, to kuwa za’a rage afkuwar matsalar tarin shara a Kano.

A lokacin da nake korafin tilin shara a garin mu, sai na tuna cewa a gaskiya matsalar tarin shara a tsakiyar al’umma ba matsala ce da ta tsaya a Kano kawai ba. A’a!

Kusan ilahirin biranen arewacin Niigeriar da na je a shekarun nan na fama da matsalar shara. Sai dai a ce wasu sun fi wasu.

Tilin shara a tsakiyar al’umma na kawo barazana kala’kala ga bil adama. Alal misali saboda dankarewar sharar da ta hada da tsummokara, leda, bawawwaki, dusa, kashin awaki, takardu, kai da duk wani abu maras amfani, wadanda akan jigba akan magudanan ruwa, sauro ke cin karen sa ba babbaka. Sakamakon wannan kuwa itace cutar cizon sauro wato Malaria a turance.

Abun da kan bani mamaki kuma shine yadda zaka ga masu suyar kifi ko balangu sun soye-soye ko gashe-gashen su a dab da tilin sharar. Kuma mutane suna ta siya ba tare da tunani hakan na iya janyo musu cuttukar kamar su amai da zawo da Thypoid ba.

Haka kuma sai ka ga yara da matasa suna tsince-tsincen robobi ko rafta – kamar yadda ake cewa a Kanon – dan siyarwa.

Idan hukuma na da laifi, suma jama’ar unguwa da gari suna da nasu laifin. Menene ya sa ba za’a hada kai, a fitar da wani tsari da zai tabbatar da jama’a ba sa zubar da shara a ko ina ba sai inda hukuma ta shata? Me yasa mutane basu damu da kiwon lafiya da tsaftar muhallin su ba?

Mai yiwuwa wasu su ce ai matsalar shara kadan ce, akwai wadanda suka fi ta girma. Amma a nawa tunanin wannan ma matsala ce musamman tun da tana barazana ga lafiyar al’umma.

Me ya kamata mu yi akan matsalar shara a biranen mu? Zan so in ji daga duk mai shawara.

6 comments:

  1. Hajia wannan shawara ai kuke da ikon bada ita domin kuke shiga kasashen da suka cigaba kuma kuna ganin yadda suke da shararsu don haka ku ya dace ku bada shawara kuma za'a fi daukarta da muhimmanci sama da wadda zamu bayar. Nagode

    ReplyDelete
  2. Salam,
    Naji dadi da kika shigar da wannan matsala a cikin blog din ki. Hakika, matsalar shara ta wuce duk yadda muke tunani a birnin Kano. Bincike da nayi (thesis) na degree na farko akan Kududdufan birnin Kano nayi, kuma na samu cewa wadannan sune manyan hanyoyin kawar da shara a kasar Hausa. Duk dai da cewa it is not the ideal way of doing it.

    ReplyDelete
  3. Hakika wannan magana mai matukar muhimmanci. Anawa tunanin ina ganin laifin yafi ta'allaqa ne ga hukuma. Dalili kuwa shine; hakika muna fama da jahilci da talauci cikin al'umar mu, wanda su kadai sun isa su juyawa mutane tunanin su daga abu mai kyau zuwa kishiyar sa. Hukuma bata damu data ilmantar da al'umma ba ko ta wayar musu da kai ta inda zaka ga marasa ilimi su suka fi yawa sosai cikin al'umar mu. In har an bawa mutane ilimi, kan su ya waye su da kansu basai ance suyi ba, zaka ga rayuwar su tana canjawa suna kokarin tsafta da kiwon lafiyar su. na gode
    Abubakar Abubakar Usman
    Kuala Lumpur, Malaysia

    ReplyDelete
  4. Hajia nikam na gane inda wannan tilin sharar take, tana kofar mata daura da masallacin idi kusa da wani gidan wanka. A gaskiya hakan gazawa ce ta gwamnati ya dace ace an kawar da ita daga inda jama'a suke domin kubuta da kamuwa da chutut tuka musamman na cizon sauro. Wani abin takaicin wannan tilin sharar na daf da babban Asibitin jiha wato Asibitin Murtala. Bama nan kadai ba akwai gurare daban daban, ina ganin dawo da gagarumin aikin nan na DA'A wato (Sanitation) domin zai rage yawaitar wannan shara a tituna da lokuna, haka kuma sai gwamnati ta tashi tsaye wajen yaki da ita musamman ta hanyar samar da kayan ayukan kauwar da ita daga daurar jama'a. Allah yay mana maganin wannan matsalar

    ReplyDelete
  5. Gaskiya ne Malam Aliyu....Haka ne ka gane wannan waje. Babban abun takaicin shine sharar tana kusa da wajen da Musulmi ke ibada. Ina hankali to tunani anan?
    Shin me ya faru ne da shirin nan na tsaftace muhalli na karshen kowanne wata? Kodayake dai yanzu sai dai a yi a kowanne mako saboda yawan jama'a a Kano ya karu.

    ReplyDelete
  6. Hajia, Wallahi ni kaina ina takaicin hanya ta biyo dani wannan mum munan guri, gashi ta cinye hanyar da mota zata wuce da hanyar mugudanar ruwa Don Allah ta yaya mutane zasu sami sukunin aiwatar dayin ibada. A gaskiya ba kowane mutum bane yasan ana gudanar da wannan shiri na da'a (Sanitation) a turance sam sam baya tasiri yanzu a hakan kuma wai anayi a duk asabar din karshen wata. Ina ganin inda za'a dawo dashi gadan gadan da bashi mahimmanci toh zamu amfana kwarai da gaske. Dafatan Allah yasa dai mahukuntan namu sun jimu, kuma zasuyi kokarin magance su. Nagode

    ReplyDelete