Monday 23 August 2010

Wasu na Shan Ruwan Bunu a Watan Azumi, Wasu na Shan Kindirmon Kwali


Watan Azumi wata ne mai alfarma ga dukkanin Musulmi a koina a cikin duniya. Kuma yau, a kwana a tashi, gashi har wata yana neman rabawa. A duk tsahon wannan watan BBC Hausa tana kawo rahotanni da sakonnin “shan ruwa daga masu sauraron mu”.

Wasu sun aiko mana da tambaya suna cewa mecece fa’ida ko hikimar kawo sakonnin “shan ruwa daga masu sauraron mu?” To lallai ga wanda bai kalli lamarin cikin zurfin tunani ba zai ga tamkar ba wani abu ba ne illa kawai kawo mutane suna cewa sun ci kaza sun sha kaza. A saboda haka kenan wannan ba abu ne mai mahimmanci ba.

Sai dai ni kuwa ba haka nake kallon abun ba. Ina kallon sa ne daga fannin launin abincin da mafi yawan jama’ar mu ke ci a wannan wata mai tsarki bayan sun kamalla ibadar su da magariba.

Kowa dai ya wuni da azumi, zai so ya yi buda baki da dan abun marmari da kuma ababen gina jiki wadanda zasu mayar da gurbin abunda aka rasa a yayin azumin. Sai dai sauraron irin abunda da mafi yawan al’ummar Hausawa ke shan ruwa da su, abu ne dake kawo hawaye a ido.

“Ni dai yau na sha ruwa da ruwan bunu da rama; yau na ci dabino da kunun kanwa, illa iyaka; ni dai na sha ruwa da dan-wake da mai da yaji, iyakar abunda Allah ya hore min kenan, Allah ya nuna mana gobe lafiya!”

Wadannan sune kadan daga dubban sakonnin da BBC Hausa ke samu a kowanne dare. Me sakonnin suke nuna mana? Lallai suna yin nuni ne da irin wahalar da jama’a suke ciki a kasar mu. Kuma yayinda miliyoyi ke shan “ruwan bunu” wasu ‘yan tsiraru kuwa suna shan kindirmon kwali mai sanyi da naman kaji.

Nigeria dai ba kasa ce matalauciya ba. Amma kuma jam’a na cikin halin matanancin talauci. An san dalilan da suke janyo talaucin: rashin shugabanci na-gari, rashawa, almundahana, rashin adalci da tsananin san-kai. Kididdgar Majalisar Dinkin Duniya na cewa mafi yawan ‘yan Nigeria na rayuwa ne akan kasa da Dala daya – wato kasa da Naira 150 - a rana.

A wannan lokaci na ibada kamata yayi mu kara tunani a game da halayyar mu ko Allah zai ji tausayin mu. Mu gyara halayen mu sannan kuma mu roke Shi Ya ba mu shugabanni masu tausayin talakawa, wadanda zasu fitar da al’ummar mu daga kangin talauci.

A sha ruwa lafiya!

6 comments:

  1. Assalm. Lalle Hajiaw wannan shiri kwarai da gaske munji dadin sa kwarai da gaske. sai dai wani hanzari ba gudu ba, anya kuwa wasu mutanan basuna aikowa bane domin raha da nishadi? ina ganin mafi akasarin wayanda ke shan wahalar rayuwa sun fito ne daga karkara amma nakanji wasu a cikin burane suna lissafo ire iren abincin da mazauna kauyuka ne kici. toh ni dai sha'warata ita ce, daku bada karfi sosai akan mazuna karkara duk da cewa a birni n ma akwai masu fama da yau kwarai da gaske. Dafatan Allah ya mana jagora yasa muna daga cikin bayin da akewa rahama a wannan wata na ramadana, ya kuma dawo da shuwaga bannin mu turbar gaskiya. Nagode AMU KWALLI KN

    ReplyDelete
  2. Assalm. Lalle Hajiaw wannan shiri kwarai da gaske munji dadin sa kwarai da gaske. sai dai wani hanzari ba gudu ba, anya kuwa wasu mutanan basuna aikowa bane domin raha da nishadi? ina ganin mafi akasarin wayanda ke shan wahalar rayuwa sun fito ne daga karkara amma nakanji wasu a cikin burane suna lissafo ire iren abincin da mazauna kauyuka ne kici. toh ni dai sha'warata ita ce, daku bada karfi sosai akan mazuna karkara duk da cewa a birni n ma akwai masu fama da yau kwarai da gaske. Dafatan Allah ya mana jagora yasa muna daga cikin bayin da akewa rahama a wannan wata na ramadana, ya kuma dawo da shuwaga bannin mu turbar gaskiya. Nagode AMU KWALLI KN

    ReplyDelete
  3. Wato matsalar rashin shugabanni masu tsoron Allah daga sama har kasa. Suma talakawa suna da nasu laifin na daukar tumasanci, cin amana da kololuwar rashin tsoron Allah a dukkan al'amurra. Najeriya na bukatar canji irin na cikin zukatan mutanenta. Amma matsalar daga ina za'a fara? A ganina sai an sami shugabannin da zasu jagorar canza zukatan mutanen Najeriya wadanda da gaske suke, kuma suma su zama zukatansu zasu iya daukar gwagwarmayar: sai an jure, kuma za'a sah wuya ba kadan ba; amma a karshe za'a sami fa'ida.

    Jibirl Lawal
    Zaria

    ReplyDelete
  4. Nagode Malamai...mu ci gaba da tattaunawa... ina karuwa sosai.

    ReplyDelete
  5. @jibrin: maganar ka haka take amma karka manta wannan kasar tamu na da dumbin arzikin da kowane talaka zai iya rayuwa akan daruruwan nerori da kwanciyar hankali da lumana, amma kayi maganar rashin shuwaga banni adalai mahandam, a nan zan iya cewa laifin na tattare damu. kamata yayi duk wani wanda bamu yarda da ingancin sa ba tun wuri mu nuna bujirewar mu gare shi, amma sai kaga talakan shine kan gaba wajen ganin azzalumin ya dare kujerar mulki kuma daga karshe kasan wa gari zai wa ya.@Hajia: wallahi kuna kokari matuka ga ya, musamman shirin nan naku RA'AYI RIGA (A H Y S) da ra'ayoyin da kuke karantowa hakan na zaburar da masu kokarin gane gaskiya. ku cigaba hajia da kokarin kune silar gyaruwar NIG. insha ALLAH. ki huta lafia. AMU KWALLI KN.

    ReplyDelete
  6. A gaskiya Haji. fito da wannan shafi da kukayi na Bbchausa facebook ya kara martabar ku a idanun duniya, kuma tasa yanzu ina ganin babu dan/ ko yar kauye. mutane da dama a kullum sun dada wayewa kuma kune silar. kasan cewa ta member a Bbc hausa facebook tun ranar da akabude kai da sauran shafuka ta sani nayi abokanai asassa daban daban na Najeria da makota, kuma akwai mutanan da a kullum ke kirana ta waya domin na koya musu yadda wannan duniyar take atafin mu, hadi da yi musu register emils, facebook. lalle sai muyiwa Allah godiya daya hadamu daku. Allah yabar zumunci. ALIYU M UMAR KWALLI

    ReplyDelete