Friday 17 June 2011

Yaya Za'a Warware Matsalar Boko Haram

Matsalar Boko Haram, matsala ce da kowa yake jin tsoron yin sharhi akai. Dalili kuwa shine suna ganin muddin suka yi magana watakila ‘yan Boko Haram din su kai masu hari. Amma kuma a matsayinmu na ‘yan jarida dole ne mu yi tsokaci dangane da abubuwan da ke faruwa a kasarmu da nufin neman hanyoyin warware wadanda muke ganin matsaloli ne.

Boko Haram ta somo asali yau kusan shekaru 2, inda ake daukar jihar Borno dake arewa maso gabashin Nigeriar a matsayin hedikwatar su. Ana ganin aikace-aikacen ‘yan kungiyar da cewa kokari ne na ganin an kaddamar da Shari’ar Musulunci a Nigeria.

Hare-haren da Boko Haram ke kaiwa sun tsananta ne bayan kashe shugabansu
Mohammed Yusuf da jami’an tsaron Nigeria suka a Yulin 2009. Tun a wancen lokacin ne ‘yan Boko Haram suka sha alwashin daukar fansa tare da yaki da duk wadanda suke ganin makiyin su ne.

Yanzu haka dai abu yayi abu. Boko Haram na kai hari ta ko ina, duk dai a kokarin cimma manufofinsu. A lokacin da ya kai ziyara Amurka, Shugaban Nigeria Goodluck Jonathan ya bayyana a makon da ya gabata cewa yana neman a tattauna da ‘yan Boko Haram din, da nufin kawo karshen tashe-tashen hankulan da ake samu a wasu sassan kasar. Sai dai bayan kalamin na sa, sai aka ambato shugaban rundunar ‘yan sandan Nigeria Hafiz Ringim yana yin barazana ga ‘yan Boko Haram yana mai cewa karyar su ta kusan karewa.

Ana dai bayyana cewa wai wannan furuci ne ya tunzura ‘yan Boko Haram suka kai hari a hedikwatar ‘yan sandan Nigeria dake Abuja. Daga bisani kungiyar ta fitar da sanarwa tana mai daukar alhakin harin bam din da yayi sanadiyyar hasarar rayuwa da dukiya.

To yanzu da aka zo wannan matsaya, ta yaya za’a tunnkari matsalar Boko Haram?

Ni dai har yanzu banga wani wanda a yanzu ya lashi takobin cewa yana da wata cikakkiyar masaniya ba. Amma a matsayin mu na masu sharhi kan al’amuran da suka shafi kasar mu wajibi ne mu nemi ansa ga wasu mahimamman tambayoyi. Wadannan kuwa sune:

Menene ya janyo matsalar Boko Haram? Su wanene ‘yan Boko Haram? Ta yaya za’a fara tattaunawa da su domin neman sulhu? Yaya shugabannin Nigeria zasu kasance masu tausayin jama’ar su ta yadda jama’a zasu daina yi musu kallon makiya? Yaya ‘Yan Nigeria suke san makomar kasarsu a gajeren lokaci da kuma a shekarun gaba ya kasance? Wadanna matakai za’a dauka na zahiri ba abunda Fulani suke cewa “foululu” kawai ba?

Bayan mun yi wadannan sai mu hada da addu’ar neman Allah ya kawo mana zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar mu Nigeria.

6 comments:

  1. ai kuwa Hajiya sai mahukuntar kasar nan tamu sun kwance damarar zalinci a zukatansu, su kuma daura ta adalici ita ce kadai hanyar samun zaman lafiya a kasar nan tamu ta Najeriya. kuma zama da Teburin sulhu da mutanan ne zai taimaka, haka kuma su kansu jami'an tsaro sai sun kiyaye lafuzan su, kamar yadda Hafizu Ringim yayi wannan kasassabar har ta jawo babban hari a offishinsa. AM UMAR KwALLI KANO

    ReplyDelete
  2. A gaskiya tsaro abune mai muhimmancin farko tsakanin jama'ah. Amma duk abinda tautaunawa ta lumana bata kawo ba, to tashin hankali ba zai kawo shi ba. Saboda haka matsalar boko haram, masalaharta sulhu ne tsakanin gwamnati da su da kuma jama'ah a daya bangare. Jama'ah musamman kamar ta Maiduguri tana da muhimmiyar rawa da zata iya takawa idan dai gwamnati za ta bata dama, ganin cewa tafi kusa da tushen kungiyar.

    Amma abin kuskure shine yadda gwamnati ke neman ci da zuci wajen farma matsalar da karfi. Ya ilahi, mutumin da ba shi da kama ta daban da sauran mutane, ta yaya za a ce a zakulo shi da karfi? Hakane yasa aka wayi gari maimakon boko haram sai gashi al'umma ce ke cutuwa abin har ya zama mutane sun shiga tsaka mai wuya, gefen boko haram zafi haka kuma ta bangaren jami'an tsaronma akuba.
    Allah Shi kyauta ya kuma bamu zama lafiya duk Najeriya.

    ReplyDelete
  3. Hajiya maganarki gaskiya ne, kuma babban abinda ya jawo wannan matsala ta Boko Haram shi ne irin yadda shugaban Nigeria ke mulkin kama karya, daga su sai yayansu. To tabbas idan ana so irin wadannan tashe tashen hankula ya ragu ko a dakushe shi a Nigeria sai lokacin da shugabanni suka dawo yin adalci ga talakawa.

    ReplyDelete
  4. Dole gwamnati ta zauna da su ta ji ra'ayinsu.Dole gwamnati ta zauna da su ta ji ra'ayinsu.

    ReplyDelete
  5. Agaskiya iya shawokan matsalar nigeria bakaramin aikibane, dafarko yazama dole shugabanni sudaina sata da zalunci sukumayi kokarin gyaramana kasa tunda dama aisune suka lalatata. Daga Mustapha Usman Gumel

    ReplyDelete
  6. Gaskiyane hajiya jamila tangaza wannan magana taki haka take.

    ReplyDelete