Friday 4 October 2013

Babban Abu Da Ya Sosa Mani Rai

Yau shekara biyu da wata uku kenan cif, rabon da na yi rubutu a wannan mattara tawa – Almajira. Na jima ne kuwa ban yi rubutun ba saboda matukar sauye-sauye na halin rayuwa ta yau da kullum. Wannan sauye-sauye kuwa sun hada da kai komo a wurin aiki da gida. Tun sanda na rubuta tunani na karshe a wannan dandali abubuwa da dama sun sauya. Babba daga cikin su shine na ajiye aikina a wajen da mutane da yawa suka fi sanina wato BBC, bayan na shafe kusan shekaru ashirin ina aiki da wannan kafar yada labaran ta Ingila mai dadadden tarihi. Dama dai Hausawa suka ce komai na duniya mai karewa in banda ikon Allah. Lallai tun sannan na komo kasata Nigeria domin gannin yadda zan ci gaba da ba da gudunmawata ga al’ummata. A yanzu haka dai ina aiki a hukumar tsare-tsaren taswirar birnin Abuja wato Abuja Geographic Information Systems (AGIS). A yau wani babban abu da ya sosa mani rai ya faru. Shugabannin kungiyar Murya Talaka, Shiyyar Jihar Kano – wato Jiha ta, sun yo tattaki, suka kawo mani ziyara. Muraya Talaka sun gabatar mani da shaidar yabo kan abunda suka kira taimakar da na yi “wajen bunkasa harshen Hausa da dabi’un Hausawa da kuma bugu da kari kusantar Talaka”. Sun yi bayani dalla-dalla a game da abunda ya sa suka ga na dace na karbi wannan lambar yabo. A takaice dai sun zayyane mani tarihi na nan take! A karshe dai matasan nan sai da suka sa na zubar da hawaye. Ashe duk abunda kake yi ana kallon ka? Na yi masu godiya, na karbi lambar yabon su. Kuma na ba su shawarwari a game da yadda na ke ganin ya kamata mu ci gaba da yin gwagwarmaya domin kare marasa karfi a kasarmu. A karshe sun bakaci na samu lokaci duk da yawan aikina, na koma rubutu a mattarar bayanai na Almajira, saboda a cewar su, suna ganin wannan waje tamkar wajen daukar darasi. Ni kuma na amsa da cewa zan kokarta. Toh, gashi kuwa cikin hakuncin Ubangiji na yi rubuta na farko a dandalin Almajira a cikin watanni 27. Alhamdulillah! A sharhina na gaba zan yi tsokaci kan Babban Taro na Kasa (National Conference) wanda ‘yan kungiyar Muryar Talaka suka nemi jin ra’ayi na, da kuma ko yana da dangantaka da talaka. Allah Ya ba mu Sa’a, amin!

2 comments:

  1. Re: Babban Abu Da Ya Sosa Mani Rai

    Lallai kam, Hajiya duk abun da dan'adam yake gabatarwa, Allah madaukakin sarki yana sane da shi tun kafin ma yagabatar dashi. Kai, hatta har "mu" mutane muna sane da al'amuran juna (abun yima shaida). Kuma shaida kyakkyawa daga bakin bayin Allah nagari, alamace ta nuna yaddar Allah (madaukakin sarki) akan bawan sa ko baiwar sa. Wanene yasani ko Hajiya Jamila Tangaza na daga cikin manyan salihan bayin nan da Allah ya kira a kur'aninsa. To idan ba hakaba, ta yaya dan adam a yau zai samu wata dama ta samun lambar yabo daga wata kungiya, amma hawaye har su zubo ma mutum, ba tare da zuciyar shi ta raya mashi cewa ya isa ne ba? Wallahi, Hajiya, mukanji dadin gudummuwar ki a shashen yada labarai na BBC Hausa- ganin fasaha da Allah yayi maki, ta gyarawa da lakanta harshen hausa a zukatan mutane irin yansamari masu tasowa kamarmu (wadanda zamani yasa ba kasafai muka lakanci wannan harshe mai albarka ba, balantana har muyi alfahri dashi).
    wallahi, dadin-dadawa, ina matukar murnar dawowarki gida domin ki bada gudummuwarki ga kasarmu Najeriya. Allah ya bamu iko mu bi tafarkin irinku-irinku, muma mudawo mu bada tamu gudummuwar, da taimakon yanuwa bayin Allah. Allah ya bada nasara a sobon aikin ki (Amin Thumma Amin)

    ReplyDelete
  2. Harma na cire rai akan wani abu zai sake faruwa a wannan shafin, mun gode Allah enzu kin waiwayo!

    Kwanakinnan bada lamban yebo ya kasance harkan siyasa da neman kudi, amma, a gaskiya wannan lamban yebo da girmamawa da kika samu, dakuma wadanda kika samu a baya, sun dace dake. Wannan yazone a lokacinda ye kamata; lokacinda kika yafe aikinki da zamanki a kasan waje kuma kika zo gida domin kibada taimako kuma da gudunmuwanki wa dubban masu bukata.

    Muna dakon ra'ayoyinki masu amfanarwa da ilmantarwa anan. Allah Ya baki sa'an gudanarda al'amuranki yedda kike fata Ya kuma baki zarafin tabbatadda manufofinki na alkhairi, ameen.

    ReplyDelete